Za ai Jana'izar tsohon Babban Hafsan Sojin Nijeriya, Lagbaja a ranar Juma'a
- Katsina City News
- 12 Nov, 2024
- 231
Idan ba a samu wata matsala ta ba-zata ba, za a binne tsohon Shugaban Hafsan Sojojin Kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, a Abuja ranar Juma'a mai zuwa.
Babban dan uwansa, Moshood Lagbaja, ya bayyana hakan a Osogbo, Jihar Osun, yayin ziyarar ta'aziyya da kungiyar tsofaffin daliban Makarantar Sakandare ta St Charles Osogbo (SCOBA) ta kai masa.
Ya ce sojojin ba za su iya sako gawarsa ga iyali ba, amma sun tabbatar za a yi masa jana’iza mai kyau a Abuja ranar Juma’a.
Wakilan kungiyar sun gabatar da wasikar ta'aziyya da Shugaban kungiyar na kasa, Tade Adekunle, da Sakatare Janar, Leye Odetoyinbo, suka sa wa hannu ga iyalin.
Da yake magana a madadin SCOBA, shugaban tawagar, wanda shi ne Mataimakin Shugaban farko, Injiniya Adesina Salami, ya bayyana marigayi Lagbaja a matsayin mutum na musamman, ɗan SCOBA mai alfahari, da kuma babban jagoran soja wanda ya yi wa ƙasa hidima da jajircewa ba tare da wani shakka ba.
Daily Nigerian Hausa