Hukumar Sufurin Jihar Katsina (KTSTA) Ta Kaddamar da Sabbin Motoci 12 Bayan Wata Tara
- Katsina City News
- 08 Nov, 2024
- 262
Katsina Times - Zaharaddeen Ishaq Abubakar
A ranar Juma’a, 8 ga watan Nuwamba, Hukumar Sufurin Jihar Katsina (KTSTA) ta gabatar wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, da sabbin motoci 12 da ta saya, a matsayin wani mataki na bunkasa aikin sufuri a jihar. Wannan sayan motocin na zuwa ne bayan da KTSTA ta gabatar da motoci guda bakwai watanni tara da suka gabata, wanda ya nuna jajircewar hukumar wajen inganta ayyukan sufuri a jihar Katsina.
A karkashin jagorancin Haruna Musa Rugoji, KTSTA ta sayi jimillar motoci 19 a cikin shekara guda da wata uku. Yayin kaddamar da motocin, Gwamna Radda ya jinjinawa nasarorin da hukumar ta samu tare da bayyana muhimmancin sufuri a cikin al’umma. "Lokacin da muka hau mulki, mun yi nazari kan kalubalen da ke fannin sufuri da kuma bukatun jama’a, wanda hakan ya sa muka samar da sabbin motoci guda 40. Yau, KTSTA ta kara da nata da ta sayi a cikin kudinta, wanda wannan babban ci-gaba ne," inji gwamnan.
Gwamna Radda ya kuma yaba wa irin jajircewar Honarabul Rugoji wajen gudanar da al’amuran hukumar KTSTA, musamman kan yadda yake gudanar da aikin hukumar cikin gaskiya da rikon amana. “Da irin wannan jagoranci, wanda muke marawa baya tare da hadin kan ‘yan majalisar jiha, mun samu cigaba mai yawa da kuma yanke shawarar da ta dace. Wannan shi ne irin jagorancin da ake bukata, kuma ina jinjina masa,” ya kara da cewa.
A jawabinsa, Honarabul Haruna Musa Rugoji ya bayyana yadda hukumar KTSTA ke gudanar da ayyukanta bisa tsare-tsare na tattalin arziki, duk da kalubalen tattalin arziki da ake fuskanta. Ya bayyana cewa, duk da tsadar mai da ake fama da shi, KTSTA ta ci gaba da yin kokari wajen tabbatar da cewa farashin motar na da araha kuma mai saukin hawa ga al’ummar jihar. “Gwamna, ka umurci KTSTA da ta saukaka farashin sufuri ga jama’ar Katsina. A sakamakon haka, farashin motocin KTSTA ya kasance mafi sauki a jihar, don tabbatar da cewa kowa na iya samun damar hawa ba tare da wata matsala ba, kamar yadda ka umurta,” inji shi.
A baya, a ranar Alhamis, KTSTA ta kaddamar da sababbin tashoshin sufuri a kananan hukumomin Mashi da Ingawa. Wadannan tashoshi na “KTSTA Mashi Substation” da “Ingawa Substation” an bude su ne domin fadada ayyukan sufuri a yankunan da ke kusa, tare da tabbatar da saukin sufuri ga al’ummar yankunan, da kuma hadin gwiwa da tsare-tsaren bunkasa ayyukan sufuri na jihar Katsina.
Wannan cigaba da KTSTA ta samu ya nuna yadda hukumar ke aiwatar da shirinta na bunkasa ayyukan sufuri, inda ta samar da karin motoci tare da bude sababbin tashoshi na sufuri. Wannan matakin na hukumar KTSTA zai kara saukaka zirga-zirgar al’ummar Katsina da kuma biyan bukatun sufuri na jihar, duk da kalubalen tattalin arzikin da ake ciki.