ASALIN SARAUTAR GALADIMAN KATSINA.
- Katsina City News
- 06 Nov, 2024
- 77
Sarautar Galadima tsohuwar Sarautace a Masarautar Katsina. Tarihi ya nuna an fara wannan Sarauta tun lokacin Sarakunan Habe, lokacin da Sarkin Katsina Muhammadu Korau ya kawo tsarin Sarautu na Gargajiya a Masarautar Katsina(1348-1398).To Sai shi Sarkin Katsina Korau (1348-1398) ya tsara manyan Hakimmai masu fada aji a fadarshi da suka hada da Gazobi, Yandaka, Samri, Galadima da sauransu. Tun wannan Lokacin Sarautar GALADIMAN Katsina take cikin manyan Hakimmai masu zaben Sarki a tsarin Masarautar Katsina.
Hakanan Kuma bayan da aka kare Jihadi a Katsina acikin shekarar 1807. An Rarraba mukamai ga Shuwagabanin Jihadi. Galadima Dudi shine mutum na farko da aka fara nadawa Galadiman Katsina Kuma Hakimin Malumfashi a cikin shekarar 1808. Galadima Dudi kanene ga Sarkin Maska Gudindi, su suka asalinsu Fulani da suka zo Katsina daga Kasar Chad, tun kamin Jihadin Danfodio. Galadima Dudi ya rasu acikin shekarar 1821, Kuma Kabarin na Nan a Unguwar Tsamiya bayan Gidan Sarkin Katsina inda aka rufe Sarakunan Musulunci na Dallazawa.
Bayan rasuwar Galadima Dudi Sai aka nada dansa watau Galadima ABDULLAHI acikin shekarar 1821. Shi Galadima Abdullahi ya auri wata Diyar Sarkin Katsina Ummarun Dallaje wadda ake Kira Magajiya Hanatari. Itace wace ta haifi SHAWAI da Sallau da Baciliye da Kuma Namoda Wanda ya kafa Sarautar Dayi a lokacin Fulani. Galadima Abdullahi yayi shekarar (40) bisa Sarauta ya rasu acikin shekarar 1861.
Bayan Galadima Abdullahi Sai dansa SHAWAI ya gajeshi acikin shekarar 1861, yayi shekara Talatin da ukku(33) Yana Sarauta, ya rasu acikin shekarar 1894.
Bayan rasuwar Sai aka nada Sallau Dan Abdullahi a Mukamin Galadiman Katsina. Sallau kuwa Sarkin Katsina Abubak ya nadashi acikin shekarar 1894. Galadima Sallau Jarumine na Gaske, yayi yake yake a lokacinsa musamman Yakin Katsina da Maradi. Yana da shekara 13 bisa gadon Sarauta Turawan Ingila suka zo Katsina acikin shekarar 1903. Kuma a zamanin da yake Galadimane aka dai dai ta tsarin mulki, aka yi rabon iyakoki a shekara ta 1915, inda aka cire Kasar Bakori, da Pawwa da Maska da Kogo daga cikin Kasar Galadima suka zama Gundumonin Hakimmai. Kuma a zamanin mulkinsane aka umarci duk Hakimman Kasar Katsina akan kowa ya koma ya zauna Garin da yake mulki, maimakon ya zauna cikin Birni tare da Sarki.
Acikin shekara ta 1923 ne Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya nada Galadiman Katsina Abubakar Dan Sallau. Shi kuwa Abubakar yayi wata daya ne bisa gadon Sarauta ya rasu. Sai Kuma Sarki Dikko ya nada Galadima Muhammadu Tunau Dan Abdullahi acikin shekara ta 1923. Galadima Tunau yayi shekara 3 ne bisa Gadon Sarauta ya rasu acikin shekarar 1926.
Bayan rasuwar Galadima Tunau Sai aka nada Galadima Adamu Wanda yayi Galadima daga shekarar 1926 zuwa 1944. Daga shi Sai Galadima Abdulmumi 1944 zuwa 1954. Acikin shekarar 1954 ne aka nada Galadima Katsina Abdullahi Sani Wanda ya rike Sarautar Galadima har zuwa shekarar 1992. Daga shi Galadiman Katsina Honourable Justice Mamman Nasir Wanda aka nada acikin shekarar 1992. Bayan rasuwar Mamman Nasir Sai Galadiman Katsina na yanzu, watau Honourable Justice Sadiq Abdullahi Mahuta.
Ita wannan Sarauta ta Galadima tana daya daga cikin Manyan Hakimmai na Katsina Masu zaben Sarki watau ( King Makers). Sannan Kuma a ranar Bikin bada Sandar Girma ga sabon Sarkin Katsina Galadiman Katsina yana buga Gwauren Tambari Sau (12).
Alh. Musa Gambo Kofar soro.