TARIHIN UNGUWAR YARI KATSINA.
- Katsina City News
- 06 Nov, 2024
- 355
Unguwar Yari ta daya cikin Unguwannin Yammacin Katsina. Daga Yamma tayi iyaka da Marnar Gangare, daga Arewa ta yi iyaka da Gambarawa, daga Kudu ta yi iyaka da Adoro. Unguwar Yari ta samo sunan ta daga 'YARI' Wanda Yana daya daga cikin Yan Majalissar Sarkin Katsina a lokacin Sarki Dikko, Kuma shine Mai kula da Gidajen Bursuna a lokacin mulkin En, e. An Gina Gidan Yari dake Unguwar Yari a shekarar 1918, bayan an ruguje Kurkukun Dantura. Amma kamin wannan Lokacin asalin wurin da Unguwar Yari take sashe ne na Sansanin Yan Sarki na Dallazawa. Daga cikin Dallazawan da suka fara zama a wurin akwai Gidan Dan Yusufan Katsina, Hakimin Bindawa. Wannan gida na Dan Yusufan tun zamanin mulkin Dallazawa yake. Anan ne Hakimin Bindawa yake sabka tareda da Jamaarsa lokacin bukin Sallah Karama Ko babba.
A lokacin da aka Gina Gidan Yarin daga cikin mutanen da suka fara zama Unguwar akwai Yarin Katsina Hassan, Wanda shine Yari na farko a lokacin Sarki Dikko. Baya ga Yari Hassan akwai Gidan Waziri Haruna, Shi wannan gida na Waziri Haruna Sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Dikko ya bashi babban wuri a Unguwar Yarin ya Gina babban Gida, inda ya zauna tare da iyalinsa, da bayinsa, da sadakansa, da barwansa, na tsawon lokaci. Daga baya sai Sarki Dikkon ya nemi Waziri da ya bada Gidan don a Gina Gidajen Gandirebobi domin su rinka kula da Gidan Yari. Haka Kuma akayi inda shi Waziri Haruna ya matsa Arewa kadan da Gidan ya sake Gina wani Katafaren Gidan. Hakanan Kuma shima babban Dan Waziri Harunan anan Unguwar Yarin ya Gina Gidansa, Wanda har yanzu Gidan na Nan.
Hakanan Kuma akwai Gidan Malam Jibril Alkali a Unguwar Yarin. Malam Jibril shine Mahaifin Dr. Lema Jibril, Daniyan Katsina. Akwai Kuma Gidan Mamman Daku Mahaifin Janar Ahmed Daku.
Akwai Kuma Gidan Yari Ammani Wanda yayi Yarin Katsina a lokacin Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo.
Abubuwan Tarihi na Unguwar Yari akwai shi Gidan Yarin kanshi. Shi wannan Gidan Yari ance duk lokacin da Sarkin Katsina ya dawo daga Sallah Idi Yana tsayawa ya shiga Gidan Yarin yayi Bursunoni waazi akan su gyara halayensu. Ance Sarki daya fara wannan al'adar shine Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (1906-1944). Baya ga Gidan Yarin akwai Kuma ofishin Wakilin Arewa a kusa da Gidan Yarin. Sauran abubuwan Tarihi na Unguwar Yarin ance akwai wata Rijiya wadda ake amfani da ita tun lokacin Mulkin Dallazawa har zuwa yanzu bata taba kafewa ba.
Alhaji Musa Gambo Kofar soro.