TARIHIN GARIN TSIGA.
- Katsina City News
- 04 Nov, 2024
- 330
TSIGA tsohon Gari ne daya kafu tun wajen Karni na Sha tara (19th century). Tarihi ya nuna wani mutum ne da ake Kira Dantagaba da abokansa guda biyar wadanda suka fito daga wani kauyen da ake wa kirari da Kai-ko kayanka a Kasar Dawakin Tofa ta Jihar Kano, sune suka kafa Garin. Lokacin da suka iso dai dai wurin da TSIGA take yanzu, suka yada Zango anan. Dama tun da jimawa wurin Zango ne na matafiya a Kan tsohuwar babbar hanyar da ta shiga daga Malumfashi ta bi ta Kafur da Yari-bori har zuwa Maska. Bayan da suka huta, suka natsu, suka lura Ashe ma wurin Yana da niima kwarai, ga fadamu da Kasar Noma Mai kyau. Sai suka yanke shawarar zaunawa wurin dindindin. Suka share wuri suka ci gaba da yin noma abinsu. Sansanu mutane suka Rika zuwa wurin suna zama tare dasu, akwana a tashi har wuri ya zama Kauye.
Da Galadiman Katsina Sallau (1894-1923) ya samu labarin wannan wuri Mai Albarka noma Sai yasa aka Gina Kasuwa a wurin. Aka Kuma Rika Kiran Kasuwar da TSIGA, saboda akwai ciyawar cicci da yawa a kusa da ita, ta hakane Garin TSIGA ya samu sunan shi.
Ta bangaren mulki, baa samu cikakken bayani akan Dagattan TSIGA kamin zuwan Turawa. Amma an samu sunan wadanda suka yi Sarautar TSIGA daga bayan zuwan Turawan Ingila har zuwa yanzu. Daga cikin Dagattan akwai Madawakin Bakori Da Bala. Daga Madawakin Bakori Dan Bala Sai Kuma Magaji Muhammadu Wanda aka nada a cikin shekarar 1928, yayi shekara ashirin da biyu Yana Sarauta ya rasu a shekarar ta 1950. Bayan rasuwarsa dansa Muhammadu ya gajeshi acikin shekarar 1950.
A shekara ta 1992 ne Garin TSIGA ya samu sabon Matsayi na ci gaba aka daukaka shi daga Garin Magaji ya koma Garin Hakimi, ya shiga cikin jerin Garuruwan Hakimman Kasar Katsina. Sunan Sarautar Hakimin TSIGA itace Jarman Katsina, Hakimin TSIGA. Da farko an fara kai Sarkin Ban Katsina Alhaji Halilu Sule a matsayin Wakilin Sarkin Katsina, Wanda ya rike Garin TSIGA na tsawon shekara biyu. Acikin shekarar 1994 ne Sarkin Katsina Alhaji Dr. Muhammadu Kabir Usman ya nada Alhaji Sule Idris Nadabo a matsayin Hakimin TSIGA na farko da Mukamin Jarman Katsina, ya shugabanci Garin TSIGA har zuwa shekarar 1995, daga nan ne aka yi Mashi canji zuwa Bakori a matsayin Makaman Katsina, Hakimin Bakori. Daga nan Sai aka tura Maharin Katsina Alhaji Muhammadu Agawa Sule a matsayin Wakilin Sarkin Katsina na Garin TSIGA, Wanda ya rike Garin har zuwa watan Maris, na shekarar 1996.
A ranar 7 ga watan Maris ne na shekarar 1996, Sarkin Katsina Alhaji Dr. Muhammad Kabir Usman ya nada Alhaji Ibrahim Muhammad a matsayin Jarman Katsina na Ii. Wanda ya shugabanci Garin na tsawon shekara 9, a rasu a ranar 24 ga watan Nuwanban shekarar 2004.
A ranar 22 ga watan February na shekarar 2005, Masarautar Katsina ta tura Barayan Katsina Alhaji Abdullahi Kofar soro a matsayin Wakilin Sarkin Katsina na TSIGA, kamin a nada Sabon Hakimi. A ranar 12 ga watan Nuwanban shekarar 2005 ne aka nada Group Captain Abubakar Bala a matsayin Jarman Katsina Hakimin TSIGA.
Alhaji Musa Gambo Kofar soro.