Faduwar da yaran da ake zargi da shiga zanga-zanga su ka yi a kotu shiri ne - Babban Sifeton Ƴansanda
- Katsina City News
- 02 Nov, 2024
- 461
Sufeto-Janar na 'Yansanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa yanke jiki da faduwa da wasu yara shida da ake zargi da zanga-zanga suka yi a kotu kafin gabatar da su a gaban alkali ya kasance wani shiri ne da aka tsara don jan hankalin jama’a ga abin da ba daidai ba.
Egbetokun ya jaddada cewa, duk da haka, an ba da taimakon likita cikin gaggawa, ya na mai bayyana cewa 'yansanda su na da alhakin kula da lafiyar wadanda suke tsare.
A ranar Juma’a, an gurfanar da mutane 76, yawancinsu kananan yara wadanda ke fama da rashin isasshen abinci, a gaban kotu dangane da zanga-zangar #EndBadGovernance. Goma sha shida daga cikinsu sun fadi kuma aka fitar dasu daga cikin kotun.
Bayan gurfanar da su, kotu ta ba kowanne yaro beli wanda aka sa a kan Naira miliyan goma. Wannan al’amari ya haifar da suka a gida da waje.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa a wata sanarwa mai kwanan wata Nuwamba 1, da mai magana da yawun rundunar Muyiwa Adejobi ya sanya wa hannu a madadin Sufeto-Janar din, Egbetokun ya tabbatar da cewa, a karkashin dokar Najeriya, wadanda suka kai shekarun aikata laifuka sun isa a hukunta su duk da karancin shekarunsu.
Ya ce, “A yau, wani abu da ba a zata ba ya faru a kotu inda wasu shida daga cikin wadanda ake zargi suka yi gaggawar fita daga kotu kuma suka yanke jiki suka fadi , suna jan hankalin kafofin watsa labarai a wani yunkuri da aka shirya don jan hankali ga abin da ba daidai ba."
"A kwanan nan rundunar ƴansanda ta ƙasa ta gurfanar da mutane 76 da ake zargi da aikata ta'addanci, cin amanar kasa da kone-kone. Wadannan Laifuka ne manya da su ka sa ake tsare da wadanda ake zargi.
"Tun lokacin da aka fara shari'ar nan, rundunar ƴansanda ta dage wajen bin ƙa'idojin Shari'a domin yi wa waɗanda ake zargin adalci," in ji shi.