Danmajalisa A jihar Katsina Shirya Taron Inganta Tsaro a Mazabun Kankia, Kusada da Ingawa
- Katsina City News
- 30 Oct, 2024
- 147
Daga Auwal Isah (Katsina Times)
An kaddamar da wani taron karfafawa da ke mayar da hankali kan rawar da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki za su taka wajen inganta tsaro a mazabun kananan hukumomin Kankia, Kusada, da Ingawa a jihar Katsina.
Wannan taro na kwanaki biyu mai taken “Inganta Tsaro Ta Hanyar Dabarun Aiki” ya fara ne a yau Laraba a Katsina, inda aka yi jawabai masu muhimmanci game da makasudin taron, bayan an gudanar da muhawara da nazari kan dabarun tsaro.
Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kankia/Kusada da Ingawa, Honorabul Yahaya Kusada, wanda shi ne uban taro, ya bayyana cewa ya shirya taron ne domin neman mafita ga matsalar tsaro da ta fara sunsunar mazabarsa. A cewarsa, ya ziyarci shugabannin gargajiya da jami’an tsaro a yankin domin tattauna matakan da za su taimaka wajen rage hare-haren 'yan bindiga da suka yi kaurin suna wajen sata da garkuwa da mutane.
Ya bayyana cewa an yi cikakken shiri tare da masarautun gargajiya, jami’an tsaro, da wakilan al’umma domin tabbatar da nasarar wannan taro da kuma samar da tsare-tsare masu inganci da za su kare rayuka da dukiyoyi.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda, wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Dr. Nasir Mu'azu Dan-Musa, ya yaba da wannan yunkuri na dan majalisar, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da goyon baya don tabbatar da ganin an inganta tsaro a fadin jihar.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Jihar, Honorabul Jabiru Tsauri; wakilan Sarkin Katsina; Hakimai; Dagattai; masu unguwanni; iyayen kasa; da kuma jami’an tsaro, wadanda suka hada hannu wajen tsara hanyoyin tsaro da za su taimaka wajen dakile ayyukan 'yan bindiga a yankin.
Taron na daga cikin dabarun hadin kai tsakanin shugabanni da al’umma domin tabbatar da tsaro, da samar da zaman lafiya ga al’ummar yankin Katsina.
Photo: Muhammad Ali Hafiziy (Katsina Times