Gwamnatin Katsina Ta Cigaba daTantance Makarantun Koyar da Aikin Kiwon Lafiya
- Katsina City News
- 26 Oct, 2024
- 449
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
Gwamnatin Jihar Katsina ta kammala kashi na biyu na tantance makarantun koyar da aikin kiwon lafiya a fadin jihar a ranar juma'a.
Wannan mataki ya biyo bayan yawaitar bude makarantun koyar da aikin lafiya ba tare da izini ko bin ka’idoji ba, ciki har da yin rijista tare da gwamnatin tarayya, samun sahalewa daga hukumomin lafiya, da kuma samar da kayan aiki da kwararrun malamai masu inganci.
Daga cikin makarantun da ake da su a jihar, makarantu 29 ne kawai suka ziyarci ma’aikatar lafiya domin tantancewa. Makarantun sun hada da guda 14 daga yankin Katsina da kuma guda 15 daga yankin Daura. Tantancewar na da nufin tabbatar da cika ka’idojin da ake bukata kafin a basu damar ci gaba da aiki.
Kwamitin da aka kafa zai ziyarci makarantun nan gaba domin tabbatar da ingancin kayan aiki da kuma cika duk sharuddan da aka gindaya. Wannan zai tantance ko makarantun zasu ci gaba da gudanar da ayyukansu na koyarwa ko a’a.