.
An haifi Aliyu Namangi a wannan kauyen ne mai suna Mangi a kusa da birnin Zariya. Hijira na da shekara dubu daya da dari uku da goma sha biyar 1315 A. H. wacce ta yi daidai da shekara ta dubu daya da dari takwas da casa 'in da hudu 1894. A, D. A ranar larabgana, wato laraba karshen watan safar wato watan biyu na musulinci. An haife shi a lokacin mulkin sarkin Zazzau Kwasau.
Kamar yadda aka ambata an haifi Aliyu Namangi lafiyarsa kalau kamar sauran jarirai. Bayan shekara daya da haihuwa a watan safar sai idanuwansa suka tsiyaye a sakamakon gamayyar cuta kyanda da ta Agana da suka same shi a lokacin daya. Wannan shi ne musabbabin makancewar Aliyu Namangi. An sha (lkaciya, kuido) Aliyu Namangi bayan ya shekara bakwai a duniya. Bayan ya warke sai aka danka shi a hannun wani Malami mai suna Malam Ibrahim domin ya karantar da shi Al Kur'ani mai girma. Fara karatunsa ke da wuya sai Malam Ibrahim ya yi kaura daga garin Mangi.
Daga nan sai ya koma wajen Malam Gambo. A wannan makaratan ya yi karatun Kur'ani har zuwa izu hudu (Wato Tabaraka.) A lokaci da Malam Gambo ya tashi yin kaura daga garin Mangi zuwa cikin birnin Zariya, bai bar Aliyu Namangi a baya ba, tare suka tafi.
Bayan da Aliyu Namangi ya kai shekara goma sha shida da haihuwa sai mahaifinsa ya yi masa kyautar wata baiwa. Da ya kai shekara ashirin da daya da haihuwa sai mahaifinsa ya yi masa auren fari. Duk da lalurar ido da kuma auren da aka yi masa, bai hana shi neman ilimi ba ba kamar sauran dalibai ba masu gani, Aliyu Namangi haddace karatunsa yake yi. A kullun sai ya kawo hadarsa kafin a dora masa sabon karatu. Duk da cewa ba ya gani shi ma ana rubuta masa ne a allo kamar sauran dalibai Idan ya mance da karatunsa sai kaninsa Abdulkadir ya tuna masa, idan ya duba allonsa. Wata ranar sai malamin da yake yi wa Aliyu Namangi rubutu a allo ya gaji bai rubuta masa ba. Wannan sura ta yi wa Aliyu Namangi wuyar hadda sai yai ta kuka. Daga baya sai malamin ya rubuta masa karatun da ya kasa haddacewa Cikin dan kankanin lokaci Allah da ikonSa sai ya haddace.
Aliyu Namangi bai tsaya kan karatun Kur'ani kadai ba ya yi karatun wasu fannonin ilimi a wajen Malamai da dama. Daga cikin littafan da ya karanta akwai kawa 'idi da Ahalari da Ishimawi da Iziyya da Risala da Askari da Muhtarsa. Bai tsaya nan ba har tafsiri sai da ya karanta da sauran littafan addini.
Aliyu Namangi neman iliminsa ba wai a Mangi ya tsaya ba ya yi tafiye -tafiye da dama domin neman ilimi. Ga jerin sunayen Malaman da kuma garuruwan wadannan Malamai. Daga cikin wadannan Malamai. Malam Muhammudu Gwandu da Malam Na'iya Zariya da Malam Ramalan Limamin Wushishi da Malam Yahuza na Zariya. da Malam Sa'idu Kusfa Zariya. da Malam Na Ta'ala Wusono da Malam Abdulkadir Banufe da dai sauran su.
Baya Wadannan malamai, wasu wadanda suka taka rawa a rayuwar Aliyu Namangi ta fannin ilimi su ne Shitawa (Zuriyar Malam Shitu Dan Abdulrauf) Domin shi da kansa ga abin da ya ke cewa a wadannan baitocin.
Ni da Shitawa na saba.
Tun gaban ban hankali ba.
Sun rike ni rikon da ba.
Duka da a kai ma shi ba.
Im ba gatansa tai yawa ba.
Shaihuna Abdurra'uf .
Tun ina yaro la'ifi.
Ya rike ni rikon nazifi.
Har ya zan na fara karfi.
Bai bar ni ciki hakukuwa ba.
Shi ya ce min Kai karatu.
Ko da ba ka ganin rubutu.
In ka gane ka wadatu.
Dubi Tahmisin Tafuttu.
Sai ban ji rabo kamar sa,ni ba.
In Allah ya yarda za mu ci gaba Har zuwa fara waken shi da rasuwar shi.