Jami'ar Napoli Ta Gudanar Da Nazari Kan Magungunan Gargajiya Na Hausawa
- Katsina City News
- 18 Oct, 2024
- 873
Jami'ar Napoli, L'Orientale ta kasar Italiya, ta karbi taron nazari kan al'adu da magungunan gargajiya na Hausawa, inda aka gabatar da wata takarda mai muhimmanci kan wannan batu. Taron ya samu halartar fitattun masana ciki har da Farfesa Andrea Brigaglia da Farfesa Bashir Aliyu Sallau, daga Katsina da Farfesa Sagio Baldi, wanda ya kafa Sashen Nazarin Hausa a wannan jami'ar.
Takardar ta yi cikakken nazari kan yadda Hausawa ke amfani da magungunan gargajiya wajen kiwon lafiya. Masana sun bayyana yadda magungunan gargajiya ke taka muhimmiyar rawa wajen lafiyar al'umma, musamman a yankunan karkara.
Farfesa Andrea Brigaglia, wanda shi ne ya gayyaci marubucin takardar domin gabatar da wannan bincike, ya kasance kwararren malami a ilimin addini da harsuna. Matar Farfesa Andrea Bahaushiya ce daga Kano, wanda ya taimaka masa wajen fahimtar al'adun Hausawa da harshensu. Ya kuma rungumi addinin Musulunci sakamakon nazarinsa kan malaman addinin Musulunci.
A matsayin malami mai koyarwa a Sashen Koyar da Larabci na Jami'ar Bayero, Farfesa Brigaglia ya yaye dalibai da dama, ciki har da Dr. Dahiru, fitaccen malami a fannin Larabci. Gudummawar Farfesa Andrea ta taimaka wajen bunkasa ilimin addini da al'adu tsakanin kasashe.
Taron ya zama dandalin fahimtar al'adun Hausawa, musamman wajen amfani da magungunan gargajiya, wanda ke da muhimmanci wajen kiwon lafiyar al'umma ba tare da dogaro kacokam kan magungunan zamani ba.