Gwamnatin Jihar Katsina Ta Tallafawa Iyalan Jami’an Tsaron Kwaminiti Wach da Suka Rasa Rayukansu a Wajen Aiki
- Katsina City News
- 13 Oct, 2024
- 138
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Alhaji Sa'idu Ibrahim Danja (Kogunan Jibiya) Mataimaki na Musamman ga gwamnan Katsina akan wadanda Ibtila'in 'Yan Bindiga Ya shafa
Gwamnatin Jihar Katsina, a karkashin jagorancin Ofishin Mai Ba Gwamnan Shawara akan Lamurran Wadanda Ibtila’in ’Yan Bindiga ya Shafa, Alhaji Sa’idu Ibrahim Danja, ta tallafawa iyalan jami’an tsaron Katsina Community Watch da suka rasa rayukansu a kwantan bauna da aka kai musu a kananan hukumomin Batsari da Danmusa.
Iyalan jami’an tsaron da suka rasa rayukansu sun samu tallafin naira miliyan ɗaya kowannensu. Haka kuma, iyalan ’yan sa-kai, wato ’yan banga wadanda ba mambobin Katsina Community Watch ba, an basu tallafin naira dubu ɗari biyar kowannensu. Haka zalika, iyalan mutanen gari da suka rasa rayukansu sun samu naira dubu ɗari biyu, yayin da aka baiwa wadanda aka kama yayin harin naira dubu ɗari.
Danja ya bayyana cewa wadanda suka samu raunuka sun karɓi naira dubu ɗari biyu, yayin da wasu da ba su cikin jami’an tsaro aka ba su naira dubu hamsin. Ya jaddada cewa, an warewa kowane rukuni na mutanen da ibtila'in ya shafa tallafin da ya dace da yanayinsu.
Bugu da ƙari, ya ce an gayyaci iyalan waɗannan marayu zuwa gidan gwamnatin jihar Katsina domin karɓar tallafin saboda dalilan tsaro. A cewarsa, akwai rade-radin cewa wasu mutane na karɓar wani kaso daga cikin kudin tallafin daga hannun waɗanda aka ba tallafin, amma ya musanta wannan zargi. Ya ce, "Bamu samu wani rahoto ba akan wannan batu, kuma idan har akwai wanda ya fuskanci irin wannan matsalar, ya kai kara domin a dauki matakin da ya dace."
Alhaji Danja ya bayyana cewa, ofishin su a bude yake ga duk wanda ke da korafi ko kuma wani batu da ya shafi wannan tallafi. Ya jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta lamunci aikata wani abu da zai bata suna ba, musamman game da waɗanda suka sadaukar da rayukansu domin kare al’umma.
A wani rahoton jaridar Katsina Times, wasu iyalai daga karamar hukumar Danmusa sun bayyana korafinsu dangane da batun karɓar kaso daga tallafin da aka basu. Sai dai Alhaji Sa’idu Ibrahim Danja ya karyata cewa hakan ba ta hanyar ofishin sa aka yi ba, kuma ya tabbatar da cewa za su dauki mataki mai tsauri akan duk wanda aka samu da wannan rashin imani.