Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Alkawarin Tallafa Wa Iyalin Sojojin Zamfara da Aka Kashe a Kwanton Bauna
- Katsina City News
- 12 Oct, 2024
- 157
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cikakken shirin gwamnatinsa na tallafa wa iyalan jami'an sojojin da aka kashe a wani kwanton bauna da 'yan bindiga suka kai musu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan jami'an sojojin da lamarin ya shafa a fadar masarautar Tsafe. Kwanton baunar da ya faru makon da ya gabata ya yi sanadiyar mutuwar jami'an tsaron, wanda hakan ya jefa masarautar da al'ummar yankin cikin alhini.
Yayin da yake nuna jajensa ga iyalan wadanda suka rasa ransu da kuma masarautar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa sadaukarwar da wadannan jami'ai suka yi ba za ta tafi a banza ba.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a Gusau, ya ambato Gwamna Lawal yana cewa: "Na zo nan yau domin in miƙa gaisuwar ta'aziyyata ga masarauta, iyalai da al'ummar Tsafe bisa ga wannan mummunan harin da ya ci rayukan gwarazanmu a wani kwanton bauna."
Ya ci gaba da cewa: "Wannan bala'i ne mai tsanani wanda muka ji radadinsa. Wannan tsayin-daka da jaruman dakarun suka yi don kare rayukan al'umma abin yabawa ne, kuma ba za mu bari hakan ya tafi haka nan ba. Na turo tawagar gwamnati ƙarƙashin jagorancin mataimakina don su gabatar da ta'aziyya ga iyalan da abin ya shafa."
Gwamna Lawal ya tabbatar wa iyalan da masarautar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da gudanar da aiki ba tare da tsayawa ba wajen kawar da 'yan bindiga daga jihar Zamfara. Ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki nauyin dukkan iyalan jami'an da suka rasa rayukansu a wannan harin.
"Na yi wannan alkawari ne a yau, kuma za mu tabbatar da cewa mun cika shi," in ji Gwamnan.
Bugu da ƙari, Gwamnan ya sanar da bayar da tallafi na kuɗaɗe da kayan abinci ga iyalan mamatan nan take.
A nasa jawabin, Sarkin Tsafe, Alhaji Muhammadu Bawa, ya bayyana godiyarsa ga Gwamna Lawal bisa ga jajircewar da yake yi wajen inganta tsaro da jin daɗin al'ummar yankin.