Babbar Kotun Tarayya Da Ke Abuja Ta Hana Kwamitin Zartarwa Cire Shugaban PDP Na Ƙasa

top-news

Maryam Jamilu Gambo, Katsina Times 

Justice Peter Lifu na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya hana Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) da Kwamitin Amintattu (BoT) na Jam’iyyar PDP su cire Umar Damagum daga matsayin Shugabanta na kasa na jam’iyyar. Wannan umarni na kotu ya hana PDP ko wani bangare daga cire shi har sai bayan babban taron jam’iyyar da aka tsara za a gudanar a watan Disamba na shekara mai zuwa.

Kotun ta bayyana cewa babu wani mutum da za a amince da shi a matsayin Shugaban PDP na kasa face Damagum har zuwa lokacin babban taron jam’iyyar. Justice Lifu ya bayar da wannan umarni ne yayin da yake yanke hukunci a wata kara da Sanata Umar El-Gash Maina ya shigar da PDP, NEC, BoT, da wasu.

Alkalin ya ce bisa tanadin sashe na 42, 47, da 67 na kundin tsarin PDP, kawai babban taron kasa na jam’iyyar ne zai iya zabar shugabannin. Saboda haka, cire Damagum daga mukaminsa kafin wannan lokaci ba zai yiwu ba. A cikin karar,  Maina, wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban PDP a jihar Yobe, ya zargi wasu jiga-jigan jam’iyyar da shirya tarurrukan sirri domin cire Damagum daga mukaminsa cikin karfin tsiya.

Maina ya bayyana cewa, tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Phillip Salawu, ne ake kokarin tursasawa domin ya maye gurbin Damagum. Maina ya kara da cewa, da zarar ya gano wannan shiri, ya rubuta takardu biyu masu dauke da koke zuwa Sakataren PDP na kasa, Samuel Anyanwu, inda ya bayyana damuwarsa kan tarurrukan sirri da ake gudanarwa. Amma duk da haka, Anyanwu bai dauki wani mataki ba, kuma ba a dauki mataki daga BoT ba.

Maina ya roki kotu da ta tabbatar da amfani da sassan 45, 47, da 67 na kundin tsarin PDP domin hana yunkurin cire Damagum daga mukamin shugaban riƙo na kasa. A cewarsa, shugabancin PDP na kasa yana juyawa tsakanin yankunan Arewa da Kudu ne, kuma babu wata hanya da za a bi wajen zaben shugaban da ta tsarin kundin jam’iyyar ba.

Bayan nazarin kundin tsarin PDP da hujjojin da aka gabatar, Justice Lifu ya yarda da bukatar Maina cewa Damagum ba zai iya rasa mukaminsa ba sai dai ta hanyar babban taron PDP ko ta umarnin kotu. Ya kara da cewa, duk wani yunkuri na soke wa’adin shekaru hudu na yankin Arewa kafin babban taron jam'iyyar zai zama cin mutunci ga kundin tsarin PDP.

Kafin wannan hukunci, alkalin ya yi watsi da hujjojin wadanda ake kara, wadanda suka yi ikirarin cewa Maina ba shi da hurumin shigar da wannan kara kuma kotun ba ta da hurumi. Justice Lifu ya bayyana cewa, tun da Maina ya nuna katin memba na PDP a gaban kotu, kuma ya dauki matakin kare kundin tsarin jam’iyyar, yana da hurumin da kuma hujjar shigar da karar.

Alkalin ya ce, Maina ya yi amfani da hakkinsa na dan jam’iyya domin ya kare tsarin da aka shimfida a kundin tsarin PDP, musamman kan kare wa’adin shugabancin yankin Arewa daga yankewa.