Adam A. Zango Ya Zama Darakta Janar A Gidan Talabijin Na Qausain TV
- Katsina City News
- 09 Oct, 2024
- 479
Katsina Times
Kamfanin Qausain Group ya sanar da nadin mashahurin jarumin Kannywood kuma mawaki, Adam A. Zango, a matsayin Daraktan Janar na tashar talabijin din Qausain TV. Shugaban Qausain Group, Alhaji Nasir Idris, ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Litinin a birnin Abuja, yana mai cewa nadin ya fara aiki nan take, kamar yadda aka tabbatar a taron kwamitin gudanarwar kamfanin.
A cewar Idris, tsohon Gwamnan Sojan Kano, Kanal Sani Bello (ritaya), shi ne aka nada Shugaban rikon kwarya na kwamitin gudanarwa na kamfanin, wanda zai yi wa’adin farko na shekaru hudu, kamar yadda dokar CAMA (Companies and Allied Matters Act) ta tanadar. "Bello zai jagoranci tattaunawa mai kyau, samar da ingantaccen shugabanci da kuma tabbatar da yanke shawara mai ma’ana a cikin kwamitin," inji shi.
Haka zalika, tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki, Farfesa Isa Pantami, an nada shi a matsayin mamba mai zaman kansa a kwamitin gudanarwa. Alhaji Idris ya bayyana cewa, "Pantami zai bayar da kyakkyawan hangen nesa da kuma yanke shawara ba tare da son rai ba, domin tabbatar da cewa duk shawarwarin kwamitin ba su sabawa manufofin kamfanin."
Bugu da ƙari, an nada tsohon babban mai watsa labarai na BBC Hausa, Ahmad Abdullahi, a matsayin mamba. Abdullahi, wanda ya yi wa BBC aiki na tsawon shekaru 28, zai kula da tabbatar da ingantaccen shugabanci da bin doka a kamfanin.
Shugaban Qausain Group ya bayyana cewa, “Abdullahi zai taimaka wajen tsara manufofin ci gaban Qausain TV, bunkasa alaka da kasuwanci, da kuma kara inganta dabarun tallace-tallace na kamfanin.”
Ya kara da cewa ya na da yakinin cewa irin gogewarsu zai taimaka wajen cimma nasarorin da kamfanin ya sanya gaba.