Taron Matasa a Jihar Katsina: an Karrama Alh. M. M. Murtala, Da gudanar da Ƙasidu akan Zaman Lafiya a Najeriya
- Katsina City News
- 23 Sep, 2024
- 355
Zaharaddeen Ishaq Abubakar Katsina Times
Majalisar Matasa ta Kasa reshen jihar Katsina (NYCN) ta shirya taron yini daya a ranar Lahadi, 22 ga watan Satumba, 2024, a dakin taro na Katsina Motel, domin tattauna batun zaman lafiya da tsaro, tare da karrama tsohon Daraktan Hukumar Jami’an Tsaro na Farin Kaya (DSS) a jihar Borno, Marafan Ruma, Alh. M. M. Murtala (ADG Rtd), da wasu fitattun mutane da suka taka rawar gani wajen ci gaban al’umma da tabbatar da zaman lafiya.
Taron ya gudana ne karkashin jagorancin Majalisar Matasa ta Kasa reshen jihar Katsina, kuma an yi shi ne da taken “Zaman Lafiya da Tsaro a Najeriya: Wajibi Na Kowa da Kowa.” Manufar taron ita ce jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin matasa da sauran al’umma wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya, tare da kara fahimtar irin rawar da matasa za su iya takawa wajen ciyar da kasa gaba.
Alh. M. M. Murtala, wanda aka karrama da lambar yabo a taron, ya samu girmamawa ne sakamakon irin gudummuwar da ya bayar wajen tabbatar da tsaro a lokacin da yake aiki da DSS a jihar Borno, tare da jajircewarsa wajen inganta zaman lafiya da tsaron kasar nan.
A yayin taron, masana da shugabanni sun gabatar da kasidu masu mahimmanci kan yanayin zaman lafiya da tsaro a jihar Katsina da Najeriya baki daya, inda aka lalubo hanyoyin da matasa da sauran al’umma za su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
Taron ya samu halartar fitattun mutane da suka hada da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Katsina, Hon. Nasir Mu’azu Danmusa, da Prof. Mukhtar Alkasim, da Dr. Ruwan Godiya, da Alh. Nura Kofar Sauri (Jakada), da Alh. Haruna Maiwada Sadaukin Kaita, tare da shugabannin matasa, jami’an gwamnati, da sauran ‘yan kasa, wadanda suka halarci taron domin yin murnar nasarorin da wadanda aka karrama suka samu.
An tattauna kan yadda zaman lafiya da tsaro ke da matukar muhimmanci a cikin al’umma, musamman a wannan lokaci da Najeriya ke fuskantar kalubale iri-iri. Haka zalika, an yaba wa kokarin wadanda aka karrama wajen jajircewarsu a fannin tsaro da ci gaban al’umma.
Taron ya kasance wani ginshiki wajen sake tunatar da al’umma, musamman matasa, muhimmancin hada kai da yin aiki tare wajen samun ci gaba mai dorewa, tare da tabbatar da zaman lafiya da lumana a cikin kasa.