Gwamna Radda Ya Karɓi Baƙuncin Tawagar Majalisar Gwajin Lafiya ta Ƙasa a Jihar Katsina
- Katsina City News
- 20 Sep, 2024
- 356
A ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba 2024, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ya tarbi tawagar Majalisar Malaman Gwajin Lafiya ta Ƙasa (Medical Laboratory Council of Nigeria) a gidan gwamnatin jihar.
Shugaban tawagar kuma Rijistaran majalisar, Farfesa Tosun Erhabor, ya bayyana cewa sun zo jihar Katsina ne don tantance shirin fara gina cibiyar horas da ɗalibai masu karatun gwajin lafiya daga jami’o’in ƙasashen waje. Cibiyar za a kafa ta ne a asibitin koyarwa na Jami'ar Umar Musa Yar'adua da ke Katsina.
Farfesa Erhabor ya ƙara da cewa cibiyar zata horar da ɗalibai kan aikin gwajin lafiya irin na gida Najeriya, musamman ma wadanda suka kammala karatu a ƙetare. Ya bayyana cewa wannan cibiya zata zama ta uku a yankin Arewa maso Yamma, bayan wadda ke Zaria a jihar Kaduna da ta Kano.
A cewarsa, "Ziyararmu zuwa ga gwamna ba kawai domin aikinmu ba ne, sai dai kuma don mu gode masa bisa kulawar da yake ba wa ɓangaren mu, inda ya bayar da dama ga kwararru masu wannan ilimi su samu manyan mukamai a ma’aikatun gwamnatin jihar."
Gwamna Raɗɗa, a nasa jawabin, ya nuna jin daɗinsa kan wannan cibiya da za a kafa a jihar Katsina. Ya kuma yabawa membobin majalisar bisa ƙoƙarin su da ya kai su samun matsayin Manyan Sakatarori a gwamnatin jihar, inda ya ce sun cika dukkan ƙa’idojin da aka shimfiɗa kafin samun nasarar jarabawar.
Gwamna Raɗɗa ya ƙara jaddada cewa jihar Katsina yanzu tana cikin jihohin da ke bai wa likitoci haƙƙin su yadda ya kamata, sabanin yadda aka saba a baya da likitoci ke kaura zuwa wasu jihohi don neman kulawa ta musamman. Ya kuma bayyana cewa, "Cibiyar da za a kafa yanzu, za ta yi aiki tare da sabuwar cibiyar gwajin lafiya da muke ginawa a asibitin Amadi Rimi, wadda zata samar da kayan aikin zamani da ake buƙata domin gudanar da gwaje-gwaje irin na ƙasashen waje."