Kungiyar Mawaƙan Asharalle Ta Ziyarci Hukumar Hisbah A Katsina
- Katsina City News
- 18 Sep, 2024
- 257
A yammacin ranar Talata Kungiyar Mawaƙan Asharalle Suka Ziyarci Ofishin hukumar Hisbah Ta Jihar Katsina Domin Tattauna Hanyoyin Kawo gyara da Tsaftace Sana'ar.
Kungiyar A Karkashin jagorancin Alhaji Ali Gwido ta Kawo Ziyarar ga Babban Kwamandan Hukumar na jihar Katsina don mika goyon baya ga Hukumar tare da neman shawarar hanyoyin tsaftace sana'ar ta Asharalle a Hukumance dubada da kalu-bale da ke cikin sana'ar da ke bukatar gyara da shawarwari.
Dakta Aminu Usman (Abu Ammar) ya nuna jin dadin ziyarar tare da bude Tattaunawar da Nasiha, Wa'azi Nuni da Fadakarwa kamar yanda ya saba, gami da kira ga resu da sauran masu sana'ar akan dora su busa saiti ba tare da take hakkokin Shari'a ba.
"Gwamnatin jihar Katsina bata kafa hukumar Hisbah don takurawa ko wata manufa ba face dora al'umma a bisa turbar da ta dace ta Addini da dawo da doka, da Ƙa'idoji na nuna da'a wa kowa da kowa." Inji shi.
A ƙarshe yayi fatan alheri da bayyana cewa kofar hukumar Hisbah a bude take ga kowa da kowa don hada hannu tare da maido da da'a, kyakkyawar dabi'a a cikin Al'umma.