Kungiyar ACDIE Ta Nemi Gwamnatin Katsina Ta Gina Hanya a Inwala
- Katsina City News
- 08 Sep, 2024
- 365
Muhammadu Ali Hafiziy, Katsina Times
Kungiyar matasa ta Action Committee for Development of Inwala and Environs (ACDIE) ta roki gwamnatin jihar Katsina ta samar da hanyoyin inganta rayuwa a unguwar Inwala. Wannan koken ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar, Yusuf Ali Madugu, wanda ya bayyana bukatar hanyoyi, makarantu, da sauran ababen more rayuwa ga yankin.
Madugu ya bayyana cewa, "Hanyar da ta fi dacewa mu nemi a gyara ita ce wadda ta tashi daga makabartar wajen makarantar Dahiru Bauci, ta bi ta wajen Kango har zuwa gidan Salale Dan Kwari, wadda zata taimaka wajen hadawa da sauran sassan unguwar."
Kungiyar ta kuma bayyana cewa, ingantacciyar hanyar zata taimaka wajen dakile ayyukan assha tare da kyautata zirga-zirgar baki a yankin. Sun kuma gode wa gwamna Dikko Umar Radda bisa jajircewarsa kan cigaban hanyoyi a fadin jihar, tare da rokon a waiwayi yankin nasu.