KIWON LAFIYA: Ciwon Tsinkau-Tsinkau (Tetanus)
- Katsina City News
- 08 Sep, 2024
- 379
15.0 Wannan cuta tana daga cikin cututtukan nan guda shida masu kashe mutane. Idan cutar ta shiga cikin jikin mutum, za ta sa shi yana yawan yin fizge-fizge.
Kwayoyin cuta ne ke haddasa wannan cutar. Wadannan kwayoyin cuta ana samun su ne a cikin kasa da kuma bayan gari (kashi). Har ila yau, wannan kwayar cutar ba ta mutuwa da wuri, tana iya rayuwa ba tare da ta shaki iska ba.
15.1 Yadda Cutar Ke Shiga Cikin Jikin Dan-Adam:
Ciwon tsinkau-tsinkau yana shiga cikin jikin dan-Adam ta hanyoyi kamar haka:
1. Ta hanyar rauni (idan an ji ciwo kuma kwayar cutar tana kusa da raunin).
2. Ta hanyar cibiyar sabon jariri, lokacin da aka yanke masa cibiya ba da tsafta ba.
3. Ta al’aurar mace yayin al’ada ko bayan haihuwa.
15.2 Yadda Cutar Ke Aiki Cikin Jikin Dan-Adam:
Cutar tana shiga cikin budadden rauni, ta zauna a gefen ciwon, sannan ta fara yaduwa a jikin mutum. Bayan ta gama yaduwa, tana sakin guba a gefen raunin. Wannan gubar tana shiga cikin jini, daga nan kuma za ta kai ga tsakiyar kwakwalwa, inda ta sa kwakwalwar ta umarci jijiyoyin jiki su fara yin fizge-fizge.
15.3 Alamomin Cutar Tsinkau-Tsinkau:
1. Cijewar haba (idan an yi kokarin bude baki ba zai bude sosai ba, kuma babu zafi).
2. Fizge-fizgen jijiyoyin fuska.
3. Fizge-fizgen jijiyoyin dake a kafofin numfashi (kamar huhun numfashi).
4. Jikin mutum zai dauke da fizge-fizge baki daya.
5. Marar lafiyar zai kasance yana gajiye kowane lokaci.
6. Ciwon kai.
15.4 Illolin Cutar Tsinkau-Tsinkau:
1. Karaya, musamman idan cutar ta kama kananan yara.
2. Rashin hankali.
3. Rashin yin numfashi yadda ya kamata.
4. Zazzabi, amma ba mai zafi ba.
5. Mutuwa.
15.5 Yadda Za a Ki Kare Kai Daga Ciwon Tsinkau-Tsinkau:
1. A kula da tsabtar abinci, jiki, da mahalli domin cutar tana rayuwa ne cikin dauda.
2. A gina rijiyoyi nesa da shadda, sannan idan shaddar ta cika, a rinka yashe ta ba tare da bata lokaci ba.
3. Kada a bar uwargida, maigida, ko ma’aikatan jinya da ungozoma su kasance ba su bada mahimmanci wajen tsaftace wajen zubar da bayan gari (kashi), saboda kwayar cutar tana rayuwa a bayan gari.
4. Idan an yi rauni ko ciwo, sai a samu kyalle mai tsafta (misali hankici) a rufe ciwon, sannan a garzaya asibiti mafi kusa.
5. Ta hanyar yin allurar riga-kafi, musamman ga mata masu juna biyu. Ana fara yi musu allurar riga-kafin idan cikin ya kai wata hudu, sai a kara yi idan cikin ya kai wata biyar, sannan a yi na karshe idan cikin ya kai wata shida. Wannan allura tana kare mai ciki daga kamuwa da wannan cutar idan ta zo haihuwa, saboda haka a kula.
15.6 Kira ga Ma’aikatan Lafiya:
Ina kira ga ma’aikatan lafiya cewa da zarar an ga mutum ya ji rauni ko ciwo, ko a gida ko a asibiti, kuma ciwon yana da alamun tsinkau-tsinkau, to a yi masa allurar (T.T) domin kare shi daga kamuwa da wannan cutar.
Kammalawa:
Ciwon tsinkau-tsinkau yana da matukar hatsari ga dan Adam, amma ana iya kare kai daga kamuwa da shi ta hanyar yin allurar riga-kafi da kuma kula da tsaftar jiki da muhalli. Allah Ya sa mu dace, Amin.
Daga Littafin Kula Da Lafiya Na Safiya Ya'u Yamel