Tatsuniya Ta 47: Labarin Marowata
- Katsina City News
- 31 Aug, 2024
- 434
Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wani mutum a wata ruga da ke gefen Dajin Ganji. Yana zaune tare da matarsa da 'ya'yansu biyu. Suna da matashin saniya guda ɗaya.
Wata rana mai gidan da matar suka yanke shawarar cewa ya kamata su yanka san nan su ci nama. Amma, su marowata ne, suna da hali na ƙin bayarwa ko da yaushe. Sai suka shirya cewa za su je daji su yanka san inda ko kuda ba za su bari ya taba naman ba.
Da zuwansu dajin, sai suka tsuguna, suka yi kashi. Nan da nan kudaje suka rufe kashin; sai suka bar wurin wannan kashi, suka je wani wurin daban suka yi wani kashin. Nan ma kudaje suka yi cincirindo a kan kashin. Da haka da haka har suka yi kashin da ba wani kuda da ya bi. Sai mai gidan ya ce: "To, a nan za mu yanka san nan."
Bayan sun yanka san, tun kafin su fede shi, sai ga wani katon zaki ya zo, sai ya ce da su: "Kai, me kuke yi a nan?"
Mai gida na jin haka sai ya ce da shi: "Mun yanka saniya ne, to amma ba mu da wutar da za mu gasa naman."
Da zaki ya ji haka sai ya ce: "To ku ba ni naman."
Duk da irin zafin rowarsu, sai suka yankar wa zaki naman suka ba shi. Amma maimakon zaki ya yi musu godiya, sai ya ce: "Ku ƙara mini zan yi muku wata waka mai dadi."
Tun ma kafin su ƙara masa, sai ya fara rera waka yana cewa:
"Dan ƙankanen abin nan, ɗungum,
Wa burga-burga ne, ɗungum,
Na buga dandane ni, ɗungum.
Aboki yana kiran aboki, ɗungum."
Da zaki ya gama wakar, sai suka sake yankar masa nama suka ba shi. Sai suka ce ya sake yin wakar su ƙara masa. Da haka da haka, har naman ya ƙare.
Suka ce da shi: "Ka ƙara yi mana waka mu ba ka ɗanmu."
Zaki ba tare da gardama ba, sai ya rera musu waka, suka miƙa masa ɗansu.
Suka ce ya kara yin wakar, za su ba shi 'yarsu. Zaki kuwa ya rera musu har ma ta fi wakokin da ya yi a baya dadi. Yana gamawa, suka danka masa 'yar makwabtansu da ta biyo su dajin saboda taya su aikin.
Can sai mutumin ya dubi zaki ya ce: "Ka ƙara yin wakar nan in ba ka matar nan tawa."
Abu kamar wasa, zaki ya yi waka, mai gida ya ba shi matarsa.
Sai kuma ya ce: "Ka ƙara yi zan ba ka kaina."
Zaki sa'a ta samu; sai ya yi wakar, mai gida kuma ya miƙa kansa ga zaki. A takaice dai, zaki ya sami uwa da uba da 'ya'ya biyu da naman saniya; sai ya kai su gidansa ya ajiye, ya tafi neman itacen da zai dafa naman san nan. Kafin ya dawo, mai gida ya kwashi iyalinsa da naman saniya sun gudu.
Bayan mai gida da iyalinsa sun yi 'yar tafiya, sai ya tsaya ya kirga su, don ya tabbatar ba a bar kowa a gidan zaki ba. Idan ya taba matarsa sai ya ce: "Daya." Ya taba ɗansa ya ce: "Biyu." Da ya taba 'yarsa ya ce: "Uku." Sai ya manta da kansa, saboda haka lissafi bai tashi daidai ba. Haka ya dinga yin wannan shirme, har wani mutum ya zo, ya ga abin da ke faruwa, sai ya ce da mai gida: "Idan na samo maka cikon mutum na huɗu lissafi ya cika, me za ka ba ni?"
Sai mai gida da matarsa suka ce: "Duk abin da ka zaɓa daga cikin abubuwan da muke da su za a ba ka."
Sai ya kirga su lissafi ya cika daidai. Daga nan sai ya dubi mai gida da matarsa ya ce: "To, ku cika alkawari."
Sai mai gida da matarsa da 'ya'yansu suka tube takalmansu, suka gyara hularsa, matar ta yi damara, 'ya'yan kowa ya shirya. Baki ɗayansu sai suka zura da gudu, suka bar mutumin yana mamaki, amma cikin raha, saboda ya ga gwanayen wauta.
Kurunkus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa:
1. Mai hankali ba ya rama mugunta da sharri sai da alheri.
2. Son kai yakan jefa mai yin sa cikin haɗari.
3. Marowaci yana iya zama tamkar dabba har ma ya cuci kansa.
4. Karshen azzalumi da-na-sani.
Mun ciro wannan labarin daga Taskar Tatsuniyoyi.