kula da Lafiya: Karumbau da bayani akansa. Hanyoyin Yadda Ake Daukar Cutar
- Katsina City News
- 25 Aug, 2024
- 414
Ana iya daukar wannan cuta ta hanyoyi kamar haka:
1. Ta hanyar taba marar lafiyar mai dauke da cutar.
2. Ta hanyar amfani da kayan wanda ke dauke da cutar.
3. Amfani da soson wanka ko tufafin mai fama da cutar.
4. Ana daukarta ta iska.
Alamomin Cutar
Ana iya gane wannan cuta ta hanyoyi kamar haka:
1. Zazzabi amma ba mai tsanani ba.
2. Kasala.
3. Rashin sha'awar abinci.
4. Kuraje waɗanda suke dauke da ruwa, kuma ana iya ganin su cikin jiki.
5. Kurajen za su fashe, ba tare da barin wata sheda ba a jiki.
6. Kurajen za su fito a kugu, fuska, da kuma kafafuwa.
7. Kurajen suna kasancewa masu matsanancin kaikai.
8. Idanuwa za su yi ja, saboda kasancewar kurajen a cikin su.
9. Rashin barci saboda kaikai.
10. A wasu lokutta mutum zai zamo bai iya yin tafiya ba saboda kasancewar kurajen a tafin kafa.
To, da zarar an ga irin waɗannan alamomi, sai a hanzarta zuwa asibiti mafi kusa domin neman magani tare da shawarwari cikin hanzari, kwana biyu da fara rashin lafiyar.
Karambau
- Kananan kwayoyin cuta ne ke kawo ta.
- Cutar tana zama cikin jikin mutum har kimanin kwanaki sha huɗu zuwa sha takwas (14-18) kafin ta fara nuna alamominta.
Banbanci Tsakanin Karambau da Cin-Zanzana
Zanzana
1. Alamomin cutar za su kasance masu tsanani.
2. An shawo kan cutar bisa doron kasa, yanzu ba a yin cin-zanzana.
3. Kuraje na fita kwana uku (3) bayan fara ciwon.
4. Yana haifar da illoli.
Karambau
1. Alamomin ba su tsananta ba.
2. Har yanzu ba a shawo kanta ba.
3. Kurajen na fita kwana daya da fara ciwon.
4. Baya haifar da wata illa.
Daga littafin Kula da Lafiya na Safiya Ya'u Yemal