‘Yan Sanda Sun Kama Masu Fashi da Makami, Satar Babura da Garkuwa da Yara a Katsina
- Katsina City News
- 21 Aug, 2024
- 443
Maryam Jamilu Gambo, Katsina Times
A cikin wasu kwararan hare-hare, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta yi nasarar ragargaza wasu kungiyoyin masu aikata laifuka da suka hada da fashi da makami, satar babura da kuma garkuwa da yara a fadin jihar, kamar yadda Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda, ASP Sadiq Abubakar, ya bayyana.
Biyo bayan rahotannin da aka samu na yawan fashi da makami a unguwar Filin Polo, Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina, karkashin jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Aliyu Abubakar Musa, ta gaggauta tura wata tawaga ta musamman domin magance matsalar. A sakamakon haka, an kama wasu fitattun ‘yan fashi da makami guda shida da suka hada da Ismail Hamza (wanda aka fi sani da Dawale), Umar Faruq Aliyu (wanda aka fi sani da Lauya), Yasir Jamilu (wanda aka fi sani da Kwame), Abu Safiyanu (wanda aka fi sani da Gije), Murtala Abubakar (wanda aka fi sani da Muri), da Bello Yusuf (wanda aka fi sani da Yellow).
A ranar 30 ga Yuli, 2024, ‘yan fashin sun kutsa kai cikin gidan Muntari Usman dauke da muggan makamai inda suka kwace masa naira miliyan daya da dubu dari takwas da hamsin (₦1,850,000). Haka kuma, a ranar 11 ga Agusta, 2024, kungiyar tare da wani abokin huldarsu, Dan Bichi, wanda har yanzu ake fako, sun sake aikata wasu fashi inda suka sace dabbobi da aka kiyasta kudinsu ya kai naira dubu dari biyu da ashirin (₦220,000) da wayoyin hannu guda biyu. ‘Yan sanda sun kwato kudaden da aka sace, dabbobin da kuma wayoyin. A halin yanzu, ana ci gaba da bincike don kama sauran masu laifin.
Kaha zalika. A ranar 17 ga Agusta, 2024, bisa sahihan bayanai da aka samu, ‘yan sanda sun kama wasu mutane guda biyar da suka kware wajen satar babura. Wadanda aka kama sun hada da Hamza Abdullahi (wanda aka fi sani da Malians) da Umar Usman, wadanda suka amsa laifin su na satar babura a masallatai yayin sallar Magriba, su raba sassan baburan su sayar. ‘Yan sanda sun kwato wani babur da kuma wasu kayayyaki da aka samo yayin bincike.
A wata sabon samame da aka gudanar a ranar 17 ga Agusta, 2024, ‘yan sanda sun ceto wani yaro dan shekara shida da aka yi garkuwa da shi a ranar 14 ga Agusta, 2024, a unguwar Kofar Sauri. Mai garkuwan, Halilu Yusuf, ya bukaci a biya shi naira miliyan biyu (₦2,000,000) a matsayin kudin fansa. ‘Yan sanda sun yi saurin daukar mataki, wanda hakan ya kai ga kama wanda ake zargin da kuma ceto yaron ba tare da wani rauni ba.
A ranar 9 ga Agusta, 2024, Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina ta kama Ibrahim Umar Gure, wanda ake zargi da satar Adaidaita Sahu a lokacin sallar Juma’a. ‘Yan sanda sun kama Gure a kan hanyar Jibia-Katsina dauke da Adaidaita Sahu din da aka sace. Wanda ake zargin ya amsa laifin kuma ya bayyana wasu abokan huldarsa, wadanda suka tsere ake akan neman su.
ASP Sadiq Abubakar ya jaddada cewa, Rundunar ‘Yan Sanda za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da cewa an gurfanar da duk masu aikata laifi a gaban kuliya.