Hukumar CSDA Ta Gudanar Da Shirin Tantance Mabukata 3,600 Da Za Su Amfana Da Tallafin Sana’o’i
- Sulaiman Umar
- 21 Aug, 2024
- 368
Daga Sulaiman Umar
Hukumar CSDA (Community and Social Development Agency) ta gudanar da taron tantance mutum 3,600 daga kananan hukumomi 12 na jihar Katsina wadanda za su amfana da tallafin inganta sana’o’i a karkashin shirin KT-CARES.
Kananan hukumomin da zasu amfana da wannan shiri sun hada da Kafur, Kankara, Faskari, Matazu, Katsina da Jibia.
Sauran sun hada da karamar hukumar Safana, Charanchi, Daura, Baure, Mashi da Kusada.
Wadannan kananan hukumomi sun kasance za su ci gajiyar tallafin ne a karo na biyu da hukumar ke yi wa masu karamin karfi da marasa galihu bayan kasancewarsu daga cikin wadanda suka amfana a karon farko da ya gudana kwanakin baya.
A jawabin shugaban cibiyar yayin tantancewar, Alhaji Muhammad Dikko Abdul’aziz ya shaida cewa saura kananan hukumomin ma za su amfana da wannan tallafi nan ba da jimawa ba sakamakon gudanar da shirin da ake daki-daki.
Shugaban kuma yayi Karin haske game da mutum 3,600 wadanda zasu amfana, a inda ya bayyana cewa an samo sunayensu ne daga ‘Social Register’ na jihar Katsina wanda aka samar da shi kimanin shekaru hudu zuwa biyar da suka shude don tabbatar da an taimakawa wadanda abin ya shafa.
Sannan shugaban yayi kira ga masu ruwa da tsaki na wadannan kananan hukumomi 12 da aka zaba da su bawa masu aikin tantancewar cikakkiyar hadin kai da goyon baya wajen ganin an aiwatar da tantancewar ba tare da wata matsala ba.
A karshe kuma shugaban cibiyar Alhaji Muhammad Dikko Abdul’aziz ya yabawa gwamna Malam Dikko Umar Radda bisa namijin kokarinshi kan sakin kudaden da hukumar ta bayar don raba tallafin a karkashin shirin KT-CARES.
CSDA dai hukuma ce wacce ta zama zakaran gwajin dafi kan aiwatar da ayyukan jin kai ga al’ummar jihar Katsina inda take gudanar da ayyuka daban-daban na jinkai ga al’ummah.
Kadan daga cikin ayyukan da wannan cibiya ke gudanarwa sun hada da ginawa da kuma gyaran makarantu, asibitoci, samar da ruwan sha ga al’ummah, tallafa wa marasa karfi maza da mata ta hanyar basu jarin sana’o’I domin dogaro da kai.
Kazalika a wannan karon ma hukumar ta yi namijin kokari wajen samar da shirin tallafawa al’ummar jihar Katsina musamman masu karamin karfi da jarin naira dubu hamsin (N50,000) ga ko wanne mutum don inganta sana’o’in su na yau da kullum.
Sannan bugu da kari hukumar ta CSDA za ta gudanar da atisa’i na koyawa wadanda za su amfana da wannan tallafi sana’o’I daban-daban a yayin shirin bada tallafin.