Tatsuniya Ta 44: Labarin Kurege Da Kura
- Katsina City News
- 18 Aug, 2024
- 308
Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana Kurege da kawarta Kura suka fita farauta. Suna cikin tafiya, sai suka tarar da inda hanya ta rabu biyu. Hanyar da ta yi dama, doguwa ce, wadda ta yi hagu kuma gajeriya. Sai Kurege ya ce da Kura:
"Tun da ke ce babba, sai ki bi doguwar hanyar, watau ta dama, ni kuma karami in bi gajeriyar, wadda ta yi hagun."
Kura ta ce: "A'a, kai karami ka bi babbar hanya, ni zan bi aramar."
Sai ya ce: "To, shi ke nan mu tafi."
Kowa ya kama hanyarsa. Kura da ta bi gajeriyar hanya ba ta sami komai ba, sai wani dan kanzo. Da lokacin da za su hadu ya matso, sai ta je inda suka shirya za su hadu da Kurege, ta tsuguna tana jira. Shi kuwa Kurege mai doguwar hanya, sai ya yi ta tafiya har ya gaji. Sai ya sami inuwar wata bishiya ya zauna yana hutawa. Da sanyin inuwa ya ratsa shi, sai ya ce:
"Kai, amma wannan inuwa da dadi take."
Sai kawai ya ji bishiya ta ce:
"Ai ma sai ka dandana ganyena ka ji irin dadinsa!"
Sai Kurege ya tsinki ganyen bishiyar nan ya sa a baki ya tauna. Sai ya ce:
"Kai, amma wannan ganye da dadi yake!"
Sai bishiya ta kara da cewa:
"Ai don ma ba ka dandana cikina ba."
Sai Kurege ya tambaye ta ya ce:
"Yaya zan yi in dandana cikinki?"
Sai ta ce:
"Idan kana so ka shiga cikina sai ka ce: `Bude bus` sai ka shiga. Idan ka ce: `Rufe kif` bayan ka sha zumar, za ta rufe."
Kurege ya yi godiya, ya matsa kusa da bishiya ya ce:
"Bude bus."
Tana jin haka sai ta tsage, Kurege ya shiga ya tarar da zuma ya zauna ya sha, har ta yi masa karo. Ya debi wata kuma ya cika jakarsa. Da ya fito daga cikin kogon bishiya, sai ya ce:
"Rufe kif."
Sai bishiya ta rufe, ya yi godiya, ya kama hanyar zuwa inda suka shirya za su hadu da Kura.
Da ya isa inda suka yi alkawarin haduwa da Kura sai ya tarar da ita tana barci. Ya shure ta, ta farka. Sai ta ga shi yana tandar baki, alamun ya ci dadi, ta tambaye shi:
"Kai, me ka samo ne mai dadi haka?"
A cikin yanga da burga, Kurege ya ce da Kura:
"Na samo wani abu ne mai dadi, ke kuma fa?"
Cikin nadama da marairaita ta ce:
"Ni kam ban samo komai ba sai wani dan kanzo. Yunwa ma nake ji. Dan ba ni abin da ka samo in dandana mana."
Sai ya ce:
"Idan na ba ki a cikin jaka, za ki cinye har da jakar, amma bari in dangwalo miki."
Kurege ya sa tsinke ya dangwalo zuma, ya mika wa Kura; ta karɓa ta sa a baki sai ta lumshe idanu da zakin zuma ya ratsa ta; sai ta cinye har da tsinken. Nan take fa sai kwadayinta ya motsa, ta ce da Kurege:
"Gaya mini inda ka samo wannan zuma mai dadi domin ni ma in je in samo."
Sai ya yi mata kwatancen bishiyar da ta ba shi zuma; Kura ta kama hanya. Da ta isa ko hutawa ba ta yi ba, sai kawai ta tsinki ganyen bishiya ta sa a bakinta. Sai dadi ya sa ta ce:
"Amma wannan ganye da dadi yake."
Da bishiya ta ji haka sai ta ce:
"Ai wannan ma kadan ne, ba ki dandana abin da ke cikina ba."
Kura ba tare da ta tambayi yadda ake shiga cikin bishiyar ba, sai kawai ta ce:
"Bude cikinki in shiga in ci dadin da kika fada."
Nan take bishiya ta bude wa Kura cikinta, ta shiga ta fara warwason zuma, tana sha. Da dadin zuma ya kwashe Kura sai ta fara wannan wakar:
"Bude bus, Rufe kif, Mu sha zaki, Kurege ba wayo, Na fi shi shan zuma, Zuma mai dadi, Ke bishiya rufe kif."
Sai ko bishiya ta rufe. Bayan wani dan lokaci sai ta ce da Kura:
"Ki yi maza ki gama, masu dakin nan fa sun kusa dawowa."
Amma saboda wauta irin ta Kura, sai ta ce da bishiya:
"Ba komai ko sun zo, ai ina da karfin da zan kore su. Idan sun gan ni ma za su gudu."
Sai ta ci gaba da shan zuma. Ta sha ta koshi, amma kuma ta manta abin da za ta fada kofa ta bude. Tana cikin wannan hali ne fa kudan suka dawo daga cin furanni. Suna shiga sakarsu da ke cikin kogon suka tarar da Kura; nan take suka far mata da harbi, tana kuka da kugi irin wanda aka san ta da shi.
Ta rude, ta rinka cewa:
"Kif, bishiya kif."
Maimakon ta ce: "Bude bus." Can dai ta yi sa'a ta ce:
"Bude bus."
Bishiya ta bude, Kura ta fito da kyar, duk jikinta ya kumbura saboda harbin zumar da ta sha; sai ta kama gudu tana hadawa da waiwaye, ta doshi inda Kurege ke jiranta.
Haka dai Kura ta koma gida tana jinya.
Da Kura ta matsa kusa Kurege ya ga yadda jikinta ya zama, sai ya nemi sanin abin da ya faru. Sai ta kwashe labari ta gaya masa; shi kuma ya ce da ita: “Kin cika mantuwa."
Kurungus
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
1. Rashin yin abu da kyakkyawar niyya shi yake sa yin nadama.
2. Yin abu da zuciya daya zai kawo taimakon Allah.
3. Hadama da rashin godiya ga Allah sukan sa a yi da-na-sani.
Mun ciro wannan labarin daga littafin
Taskar Tatsuniyoyi Na Dakta Bukar Usman.