UNICEF Ta Haɗa Hannu da Jihar Katsina Don Taimakawa Matasa Kan Yaƙi da Sauyin Yanayi
- Katsina City News
- 17 Aug, 2024
- 200
UNICEF Ta Haɗa Hannu da Jihar Katsina Don Taimakawa Matasa Kan Yaƙi da Sauyin Yanayi
Ofishin UNICEF na shiyya dake Kano ya ɗauki matakin tallafawa Jihar Katsina wajen magance matsalolin da suka shafi sauyin yanayi da kuma canza sharar roba zuwa kayan amfanin yau da kullum. Wannan shiri wani ɓangare ne na ƙoƙarin rage tasirin sauyin yanayi a yankin.
Jami’ar shirin WASH na UNICEF, Mrs. Stella IFY Terver, ta bayyana cewa UNICEF ta haɗa kai da Ma’aikatar Matasa da Cigaban Wasanni ta Jihar Katsina don tsunduma matasa cikin yaƙi da sauyin yanayi da kuma kawar da yin bayan gida a fili. Ta bayyana hakan ne a lokacin wani taro da aka yi da ƙungiyoyin matasa 30 da ke da membobi 90 a Jihar Katsina a dakin taro na sakatariyar jiha a ranar Laraba 14 ga Agusta 2024.
A yayin taron, Mrs. Stella ta bayyana cewa manufar taron ita ce wayar da kan matasa kan yadda za su kare muhalli daga haɗarin sauyin yanayi da kuma sarrafa sharar roba yadda ya dace. Ta kuma jaddada muhimmancin samar da muhalli mai ɗorewa ta hanyar shuka bishiyoyi da kuma kula da su har su girma.
A nasa jawabin maraba, Sakatare na Dindindin na Ma’aikatar Matasa da Cigaban Wasanni, Alhaji Mika'il Surajo Muhammad, ya bayyana godiyarsa ga ƙoƙarin UNICEF na tabbatar da muhalli mai kyau. Ya kuma yi alkawarin bayar da dukkan goyon bayan da ake buƙata domin samun nasarar shirin.
Bugu da ƙari, Daraktan Cigaban Matasa, Malam Sani Yahaya, ya yi bayani kan hanyoyin da ake bi don yin rijistar ƙungiyoyin matasa don cika ƙa’idodin da UNICEF ta shimfiɗa, domin tabbatar da cewa sun shirya tsaf don shiga cikin wannan muhimmin shiri.