Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Zargin Ware Biliyan 19.3 Don Kayan Kicin
- Katsina City News
- 12 Aug, 2024
- 183
Gwamnatin Jihar Zamfara ta karyata zargin da aka yi mata na ware Naira biliyan 19.3 don sayen kayan kicin a shekarar 2024, tare da bayyana cewa wannan rahoton ƙarya ne da aka ƙirƙira domin karkatar da hankalin jama'a.
Wata kafar sadarwa ce ta wallafa labarin a ranar Talata, inda ta yi zargin cewa an ware wannan adadin kuɗi a cikin kasafin kuɗin 2024 na Jihar Zamfara don sayen kayan kicin da wurin cin abinci.
A martanin da ya mayar yayin wani taron manema labarai a Gusau, Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsare, Mallam Abdulmalik Gajam, ya nuna matuƙar damuwarsa kan wannan rahoto da ya ce ƙarya ce tsagwaronta. Ya kuma yi bayanin dalla-dalla kan yadda aka tsara amfani da waɗannan kuɗaɗe.
Mallam Gajam ya bayyana cewa kuɗin Naira biliyan 19.3 da aka ware, sun shafi manyan ayyuka ne a ma’aikatar ilimi, ciki har da shirin AGILE, gina makarantun Firamare na yanki, samar da makarantar Firamare ta musamman a Gusau, da kuma sayen kayan kicin da na dafa abinci ga duk makarantun gwamnati akan Naira miliyan 40. Ya ƙara da cewa waɗannan ayyuka ne suka haɗu suka tara kuɗin.
Kwamishinan ya jaddada cewa gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta zo ne domin tabbatar da adalci wajen kashe kuɗaɗen gwamnati da kuma dakile duk wani ɓarnatar da dukiyar al'umma. Ya ce, "Ba za a taɓa samun gwamnatin mu cikin irin wannan rashin iya aiki ba."