An Kaddamar Da Rigakafin Cizon Sauro Zagaye Na Biyu A Jihar Katsina
- Katsina City News
- 09 Aug, 2024
- 386
A ranar Juma'a, 09 ga Agusta, 2024, Kwamishinan Lafiya na Jihar Katsina, Hon. Musa Adamu Funtua, ya kaddamar da zagaye na biyu na rigakafin cizon sauro a asibitin MCHC Kofar Guga da ke birnin Katsina.
Kwamishinan ya taya masu gudanar da aikin rigakafin fatan alheri, tare da tabbatar musu da cikakken goyon baya da hadin kai wajen tabbatar da nasarar aikin a fadin jihar Katsina.
An samu halartar shugaban hukumar kula da lafiyar matakin farko na jihar Katsina, Alh. Shamsu Yahaya, Dr. Ismail Buhari da wasu manyan shugabannin aikin rigakafin da sauran masu ruwa da tsaki.