Tallafi: Ya Kamata Tinubu Ya Binciki Kuɗaɗen Da Ya Ba Gwamnoni – Sheikh Yakubu
- Katsina City News
- 09 Aug, 2024
- 457
Daga EL-ZAHARADEEN UMAR, Katsina
Shugaban ƙungiyar Izala ta Kasa reshen Jihar Katsina, kuma mamba a majalisar shari'a ta ƙoli, Sheikh Yakubu Musa Hassan (Sautis-Sunnah) ya yi kira ga Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu ya binciki kuɗaɗen abinci da ake bai wa gwamnonin jihohi domin su raba wa talakawa.
Sheikh Yakubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi manema labarai a gidansa ke Katsina dangane da zanga-zangar yunwa da matsin rayuwa da matasa ke ci gaba da yi a wasu jihohin Najeriya.
Shehin Malam ya ƙara da cewa gaskiyar magana ita ce, wannan taimakon da shugaban ƙasa yake bayarwa baya kai wa ga talakawa, wanda domin su ne ake ba da kuɗaɗen da kayayyakin abincin.
Haka kuma ya yi kira ga waɗanda aka dorawa amanar kuɗaɗen, musamman gwamnonin da su ji tsoron Allah wajen rabon tallafin da gwamnatin tarayya ke basu.
“Ina kira ga 'yan siyasa da ka da su riƙa boye abincin da ake ba su, suna siya da shi, ina so ku sani, hatta ayyukan tituna da kuke yi idan yunwa ta kashe mutane wa za ku yi wa aikin?” in ji shi.
A cewarsa, a irin wannan yanayi da ƙasa da al'umma suka tsinci kansu, ya kamata a debo kuɗi daga ko'ina ne domin a magance wannan matsala ta yunwa da matsin rayuwa da jama'a ke fama da ita.
Kazalika, Sheikh Malamin ya ce duk gwamnan da aka bai wa irin wannan kuɗaɗen da kayan abinci domin a fid da al'umma daga cikin wannan kangi na yunwa da bala'i, to su ji tsoron Allah su isar da wannan saƙo ga waɗanda abin ya shafa.
Da juya kan batun zanga-zanga da ke ci gaba da gudana a wasu yankuna na ƙasar, Malamin ya ce akwai takaici irin yadda matasa suka koma barayi suna kwashe duniyoyin al'umma da sunan zanga-zanga.
Saboda haka ya yi kira ga jami'an tsaro da su tabbatar sun kama duk wanda ya taɓa kayan jama'a domin gurfanar da shi a gaban ƙuliya.
Shugaban ƙungiyar Izala ya ƙara jaddada cewa lallai ya kamata gwamnatin tarayya da kuma na jihohi da sake karatuwa ta nutsu kan batun matasa nan, a yi sabon tunani game da makomarsu ta hanyar fitowa da sabbin tsare-tsare na gwamnatin domin koya masu sana'a da ba su jari.