Gwamnatin Zamfara Ta Biya Haƙƙin Ma'aikata Sama da Naira Biliyan 7

top-news

Gwamna Dauda Lawal ya samu nasarar biyan haƙƙin ma'aikatan jihar Zamfara da na ƙananan hukumomi waɗanda suka bar aiki, wanda ya kai fiye da Naira biliyan bakwai.

A watan Janairun wannan shekarar ne gwamnatin jihar Zamfara ta kafa wani kwamitin da zai tantance tsaffin ma'aikatan jihar da ba a biya su haƙƙin su na barin aiki ba, tsakanin shekarar 2015 da 2024, da kuma bashin fanshon tsaffin ma'aikatan ƙananan hukumomi na tsakanin shekarar 2012 da 2019.

A cikin sanarwar da ya fitar yau a Gusau, Kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa an samu nasarar biyan bashin kuɗi N7,345,674,918.42 zuwa yanzu.

Sanarwar ta ƙara haske da cewa wannan aiki na biyan basussukan tsaffin ma'aikatan yana tafiya ba tare da wata tangarɗa ba. 

Ya ce, “Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta jajirce don ganin ta kammala biyan bashin tsaffin ma'aikatan jihar da na ƙananan hukumomi wanda ya kai fiye da Naira biliyan 13.

“Abin takaici ne yadda gwamnatocin da suka gabata suka bar tsaffin ma'aikatan cikin mawiyacin hali na ƙin biyan su haƙƙokin su na barin aiki, wanda yanzu Gwamna Lawal yana sallamar su.

“Yanzu dai waɗanda aka tantance su 1,926 daga cikin mutum 3,880 an biya su haƙƙoƙin su a biya bakwai da aka yi, wato kashi na 1 zuwa 6, an biya su abin da ya kai tsabar kuɗi har N3,345,642,807.22, daga cikin N8,095,948,906.63 da ake bi.

“Kwanan nan ne aka biya kashi na bakwai, waɗanda suka kai su 215, wanda ya kai ma N499,886,578.77.

“A ɗaya ɓangaren kuma, an biya tsaffin ma'aikatan ƙananan hukumomi da malamai su 3,513 a kashi na bakwai, wanda ya kai N3,500,145,532.43.

“Za a ci gaba da wannan ƙoƙari, domin yana daga cikin shirin gwamnati na inganta harkar aikin gwamnati a jihar, don samar da ingantaccen aiki.”