Kiran Minista Idris ga ’yan Nijeriya: Ku guje wa zanga-zanga, ku yi amfani da damarmakin da gwamnatin Tinubu ta samar

top-news

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi amfani da damarmakin da gwamnatin Shugaba Tinubu ta samar masu maimakon gudanar da zanga-zanga.

Ministan ya bayar da shawarar ne a taron manema labarai na duniya da ya gudanar a Abuja ranar Laraba.

Ya yi nuni da cewa cikin shekara ɗayar da ya yi a kan karagar mulki, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taka rawar gani wajen aza harsashin gina Nijeriya da za ta kasance mai ƙarfin tattalin arziki domin amfanin ‘yan ƙasa.

Ministan ya ce, “A cikin shekara ɗaya a kan karagar mulki, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taka rawar gani wajen aza harsashin gina Nijeriya da za ta kasance mai ƙarfin tattalin arziki, wadatacciya, kuma mai tsaro. Don haka, ƙarfin da aka yi amfani da shi wajen shirya ‘ zanga-zangar ƙasa’ zai fi kyau a yi amfani da shi wajen duba damarmaki da dama da gwamnatin Tinubu ta samar wa ’yan Nijeriya.

“Yin watsi da tsare-tsaren gwamnati na yanzu ta hanyar yin zanga-zanga kawai yana nuna gazawar masu shirya zanga-zangar su amince da yanayin da ake buƙata don samun cigaba; a Nijeriya kuma, sake fasalin tsarin tattalin arzikin mu, samar da manyan ababen more rayuwa, saka hannun jari a fannin lafiya, aikin gona, ƙarfafa ɗan'adam ta hanyar lamunin ɗalibai, da dai sauran su.

“Ɗaya daga cikin muhimman cigaban da aka samu bayan cire tallafin man fetur - wato canjin makamashi daga man fetur zuwa iskar gas na CNG don motoci da sauran injina - ya samar da damarmaki da dama ga 'yan Nijeriya.

“Shirin Shugaban Ƙasa na CNG zai rage wa ‘yan Nijeriya farashin sufuri da kusan kashi 50 cikin ɗari, yayin da kuma zai buɗe babbar fa’idar da ƙasar ke da ita a fannin iskar gas. Cibiyoyin musayar CNG suna ƙaruwa sosai a duk faɗin ƙasar, suna samar da ƙarin ayyukan yi.

“Tun bayan da aka ƙaddamar da shirin a bara, mun ga zuba hannun jarin sama da dalar Amurka miliyan 50 na kamfanoni masu zaman kan su wajen kafa ababen canjin CNG da samar da makamashin a duk faɗin ƙasar. Ya kamata ‘yan Nijeriya su shiga cikin wannan fanni na samar da arziki.”

Idris ya ƙara da cewa, “Gwamnatin Tarayya ta kuma samar da kayayyaki 30,000 domin sauya motocin kasuwanci masu amfani da man fetur 30,000 zuwa injina masu amfani da CNG kyauta nan da kwanaki 90 masu zuwa. 

"Kazalika, rukunin farko na bas-bas masu amfani da CNG da Gwamnatin Tarayya ta sawo domin rabawa a jihohi 36 da Gundumar Babban Birnin Tarayya sun iso.

“Don ci gaba da shawo kan tasirin cire tallafin man fetur, gwamnatin Tinubu ta gabatar da Shirin Bayar da Tallafi da Lamuni na Shugaban Ƙasa, tare da bayar da tallafin naira 50,000 a ƙarƙashin ɓangaren Tallafin Naira Biliyan 50 na shirin, kuma yana ci gaba da gudana. Ya zuwa yanzu, sama da ‘yan Nijeriya 600,000 ne suka samu tallafin naira 50,000 a faɗin Ƙananan Hukumomi 774.

“Haka zalika, za a fara bayar da lamunin naira biliyan 150 na Matsakaita da Ƙananan Sana’o’i (MSME) da Ƙera Kayayyaki bayan kammala matakin ƙarshe na tantancewa, nan da watan Agusta. Ana sa ran lamunin MSME zai ƙarfafa masana'antu kuma ya kamata 'yan Nijeriya su yi amfani da damar. 

"Yunƙurin Shugaba Tinubu na kyautata jin daɗin ma’aikatan Nijeriya ya bayyana a cikin amincewar da ya yi da sabon mafi ƙarancin albashi na naira 70,000 da Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da shi kuma ta miƙa wa Shugaba Tinubu wanda ya amince da ƙudirin (yanzu doka ce).

“A wannan karon, za a sake duba mafi ƙarancin albashi a duk bayan shekaru uku don daidaita sababbin yanayin tattalin arziki da yanayin rayuwa tare da albashin ma’aikata.

"Idan za a iya tunawa, mafi ƙarancin albashin ma’aikata na ƙasa da za a daina biya nan ba da daɗewa ba naira 35,000 ne, wanda yanzu ya ƙaru da sama da kashi 100.

“Domin a gaggauta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata, Majalisar Dokokin Ƙasar ta kuma amince da ƙarin kasafin kuɗi naira tiriliyan 6.2 da Gwamnatin Tarayya ta aika mata, wanda daga ciki za a kashe kimanin naira tiriliyan 3 domin biyan mafi ƙarancin albashi da ƙarin albashin da za a biya a ƙarƙashin sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa.

“Babu shakka, wani babban tarnaƙi da Nijeriya ke da shi wajen ci gaban tattalin arzikin karkara shi ne rashin samun kason kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya da zaɓaɓɓun Ƙananan Hukumomin ke yi cikin sama da shekaru 20, don haka ne Shugaba Tinubu ya yi yunƙurin aiwatar da ‘yancin cin gashin kan Ƙananan Hukumomi ta hanyar tuntuɓar Kotun Ƙoli domin yanke hukunci. 

"Wannan ya shaida cewa yadda gwamnatin sa ta himmatu wajen sake fasalin ƙasar, da ƙarfafa harkokin mulki da cigaba a ƙananan hukumomi, da kuma samar da ingantaccen aiki wanda a da ake wa riƙon sakainar kashi a Ƙananan Hukumomin.”

Ministan ya jaddada cewa tare da ƙarfafa wa hukumomi, Ƙananan Hukumomin za su shaida sauye-sauyen zamantakewa da tattalin arziki da ba a taɓa yin irinsa ba.

Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta tabbatar da an aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli kamar yadda aka ayyana.

“Babu shakka, gwamnatin Tinubu ita ce gwamnatin da ta fi dacewa da matasa a tarihin Nijeriya, tare da tsare-tsare da za su dace da tsarin kasuwanci na matasan Nijeriya.

“Ɗaya daga cikin hanyoyin da suka fi dacewa wajen sauƙaƙa nauyin biyan kuɗin karatun manyan makarantu a kan iyaye shi ne sabon Lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFund), tare da isasshen kasafin kuɗin da zai iya ɗaukar ɗalibai miliyan biyu.

“Asusun yana aiki tare da ba da cak ɗin kuɗi ga wasu masu cin gajiyar wanda baya ga kuɗin makaranta, kuma suna karɓar kuɗaɗen kashewa. Ya zuwa yanzu, sama da ɗalibai 110,000 ne ke nema. 

"Za a sanya wa duk waɗanda suka yi nasara sababbin shiga makaranta kuɗaɗen ba tare da ɓata lokaci ba.

"A wannan lokacin, yayin da akwai sauran abubuwan da za a ce game da nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu, zan so in dakata a nan domin babban baƙon mu, Mai Girma Sanata George Akume, Sakataren Gwamnatin Tarayya, shi ma ya tofa albarkacin bakin sa."
Daga shafin zuma Times Hausa