Zanga-Zanga: Rundunar Gidajen Gyaran Hali ta Katsina Ta Ƙara Tsaurara Matakan Tsaro
- Katsina City News
- 31 Jul, 2024
- 467
Maryam Jamilu Gambo Saulawa, Katsina Times
A cewar umarnin Shugaban Hukumar Gidajen Gyara na Halliru Nababa a cikin saƙon rediyo na ranar 23 ga Yuli, 2024, dangane da shirye-shiryen zanga-zangar ƙasa baki ɗaya kan matsalolin tattalin arziki, Konturolan Gidajen Gyaran hali na Jihar Katsina, CC Muhammad Abdulmumin Haruna, ya bayyana cibiyoyin gyara guda 12 a fadin jihar a matsayin "Wurin da za'abi bawa tsaro kamar yadda gwamnatin tarayya ta umarta.
Haka kuma, CC Abdulmumin ya tura jami'an hukumar da na sauran hukumomin tsaro zuwa cibiyoyin gyara daban-daban a cikin rundunar. Ya kuma umurci jami'an leken asiri da su bayar da rahoto mai kyau da lokaci kan duk wani cigaba da zai iya tasowa a ciki da wajen cibiyoyin. Bugu da kari, an tura ma’aikatan K9 da na sashen makamai zuwa wuraren da suka dace.
Haka zalika, ana gudanar da atisayen shawo kan tarzoma da atisayen yaki da satar mutane a duk cibiyoyin gyaran hali a cikin rundunar.
Daga ƙarshe, ya yi kira ga dukkan ma’aikata da su kasance masu sa ido, kula da tsaro da kuma aiki tukuru domin bunkasa tsaron ƙasa.