Zanga-zanga: Gwamnatin Katsina Ta Kira Taron Masu Ruwa da Tsaki
- Katsina City News
- 29 Jul, 2024
- 558
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Katsina, 28 ga Yuli, 2024 - A ranar Litinin, Gwamnatin Jihar Katsina ta gudanar da taron gaggawa na masu ruwa da tsaki da jami'an tsaro, karkashin jagorancin Gwamnan Riƙo kuma Mataimakin Gwamnan Jihar, Alhaji Faruq Lawal Jobe. Taron ya mayar da hankali ne kan shirye-shiryen zanga-zangar kasa baki daya da aka tsara yi a ranar 1 ga Agusta.
Taron ya hada da tattaunawa da wakilan wasu kungiyoyi da al'umma daga bangarorin matasa, kungiyar direbobi, 'yan kasuwa, dillalan man fetur, kungiyar muryar talaka, da kungiyar "Nigeria First, Katsina First". Dukkaninsu sun amince cewa babu bukatar gudanar da zanga-zanga a Jihar Katsina.
Kungiyoyin sun yi nuni da cewa zanga-zanga ba ta haifar da komai sai rashin zaman lafiya da tada hankalin jama'a, suna bada misalai da abinda ke faruwa a wasu kasashen duniya kamar Kenya.
Kungiyar 'yan kasuwa ta jaddada aniyar cigaba da gudanar da kasuwancin su kamar yadda suka saba, tare da rokon hukumomin tsaro da su basu kariya a wuraren kasuwancin su. Haka kuma, kungiyar direbobi ta N.U.R.T.W ta tabbatar da rashin goyon bayan zanga-zangar.
Bisa wannan matsaya ta kungiyoyin da suka wakilci al'ummar Jihar Katsina, Gwamnatin Jihar karkashin jagorancin Acting Governor, Alhaji Faruq Lawal Jobe, ta bayar da shawarar a tunkari matsalolin tsaro da addu'o'in neman sauki.
Gwamna Jobe ya bayyana irin kokarin da Gwamnatin Jihar Katsina da ta Najeriya ke yi wajen ganin al'ummar kasa sun samu saukin rayuwa, yana mai jaddada wasu muhimman tallafi da gwamnatin jihar ta bayar na shinkafa, tallafin kudi, da na takin zamani.
Jobe ya ce, "Mu mutanen Katsina zamu fito mu gudanar da addu'o'in neman zaman lafiya kamar yadda muka saba a duk watan sabuwar shekarar Musulunci wadda muka sawa suna 'Yaumul Shukr'".
A karshe, ya yi fatan alheri da zaman lafiya mai dorewa a fadin Jihar Katsina.
Taron ya samu halartar jami'an tsaro daga Civil Defence, Rundunar Sojin Najeriya, jami'an tsaron farin kaya, da 'yan sandan Jihar Katsina. Kwamishinan 'yan sanda na jiha ya yi kira ga zaman lafiya tare da rokon cewa duk wanda zai fita zanga-zanga ya tabbatar ya bayar da suna da lambar tuntuɓar sa don samun cikakkiyar kariya daga hukumomin tsaro.