Kwalejin Ilimi ta Tarayya Katsina Zata Gudanar da Taron Kammala Karatu na 2007 zuwa 2023 Shugaban Kwalejin Ya Bayyana Nasarori da Kalubale
- Katsina City News
- 26 Jul, 2024
- 514
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Katsina, 25 ga Yuli, 2024 – Kwalejin Ilimi ta Tarayya Katsina, karkashin jagorancin Dr. Aliyu Idris Funtua, FIICA, FICA, FCPS, MNAE (Wakilin Malaman Katsina), ta gudanar da taron manema labarai na bikin kammala karatu na 27-43, da zata yi, inda aka bayyana kyawawan nasarorin da kwalejin ta samu tare da kalubalen da ta fuskanta.
A jawabinsa, Dr. Funtua ya yi maraba da Shugaba da mambobin Kwamitin Gudanarwa, manyan jami'ai na kwalejin, mambobin hukumar gudanarwa, ma’aikata da dalibai, da kuma baki na musamman daga sassa daban-daban. Ya yi godiya musamman ga manema labarai bisa goyon bayan da suke bai wa kwalejin tare da yada labaranta.
A cikin jawabin nasa, Dr. Funtua ya bayyana godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa damar da aka ba su don gudanar da wannan taron. Ya tuna da burin da ya sanya a zuciyarsa lokacin da ya hau kujerar shugabanci a shekarar 2016, na ciyar da kwalejin gaba don ta zama daya daga cikin kwalejojin ilimi mafiya inganci a duniya da ake darajawa saboda nagarta a fannin koyarwa, bincike, da ayyuka. Dr. Funtua ya bayyana cewa yana farin cikin samun goyon bayan ma’aikata da dalibai wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaban kwalejin.
Lokacin da ya hau mukamin shugabanci, Dr. Funtua ya tarar da wasu manyan kalubale da suka hada da:
1. Shekaru hudu na karin girma da ba a aiwatar ba
2. Bashin kudaden karin girma da PPA
3. Rashin hadin kai da rarrabuwar kawuna
4. Karancin kudaden shiga na cikin gida (IGR)
5. Gine-ginen da suka lalace
6. Rashin isassun dakunan karatu da rumfunan taro
7. Rashin isassun ma’aikata da nauyin aiki mai yawa
8. Ƙarancin biyan ma’aikatan kwangila
9. Rashin cibiyar kammala karatu da dakin hukumar gudanarwa mai kyau
10. Rashin hanyoyi masu kyau a fadin kwalejin
11. Ayyuka da ba a kammala ba
12. Katangar kwalejin da ta lalace da kuma wacce ba a kammala ba
13. Laburare da ba shi da kayan aiki
14. Dakunan ma’aikata da ba su da kayan aiki da ba su da yawa
15. Rashin Isassun Magunguna
16. Rashin dakin CBT da kayan aikin ICT da ke lalacewa
17. Jinkirin biyan hakkoki
18. Dakin koyar da harsuna da aka gaza zamanantarwa
"Duk da wadannan kalubale, kwalejin ta samu cigaba sosai a fannonin ilimi, kayan aiki na ICT, kasuwanci, tsaftar muhalli, gaskiya, gine-gine, dakunan ma’aikata masu kyau, kayan wasanni da nishadi, dakunan kwana masu kyau ga dalibai, nagartaccen aiki, sakamakon jarrabawa a kan lokaci, da kuma nasarorin da kwalejin ta samu a fannonin daban-daban." Inji shi.
Dr. Funtua ya bayyana cewa dukkan shirye-shiryen ilimi na kwalejin sun sami cikakken sahalewa daga Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi (NCCE), yayin da shirye-shiryen digiri da ake yi tare da Jami’ar Bayero, Kano, su ma sun sami sahalewa daga Hukumar Jami'o'i ta Kasa (NUC). Ya kuma bayyana cewa a cikin dan kankanin lokaci, kwalejin za ta fara gudanar da shirye-shiryen digiri ba tare da haɗin gwiwa da kowace jami'a ba tare da shirye-shiryen NCE.
A cikin godiyarsa, Dr. Funtua ya godewa duk wanda suka tallafa wa kwalejin tun daga lokacin da ya hau mukamin shugabanci a watan Agustan 2016. Ya godewa tsoffin baki da na yanzu, ministocin ilimi na baya da na yanzu, ma’aikatan ma’aikatar ilimi ta tarayya, sakataren zartarwa na NCCE, da kuma hukumar TETFund bisa tallafin kudade da gine-gine. Ya kuma godewa Gwamnan da gwamnatin jihar Katsina bisa goyon bayan su.
Ya godewa tsohon Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Kwalejin, Dr. Danjuma Sulai, OON, da kuma tsoffin mambobin kwamitin. Ya godewa duk mambobin kwamitin bisa gudunmawar su wajen ciyar da kwalejin gaba. Haka kuma, ya godewa mambobin hukumar gudanarwa, kungiyar tsofaffin dalibai, ƙungiyoyin ma’aikata (COEASU, SSUCOEN, da NASU), da kuma Kungiyar Dalibai. Ya godewa Sarakunan gargajiya da majalisun sarakuna, da kuma hukumomin tsaro bisa zaman lafiya da aka mora a kwalejin.
A karshe, Dr. Funtua ya mika godiya ga dukkan al'ummar kwalejin da abokanta wadanda suka bada lokaci da kudin su wajen tallafawa wannan shugabanci.