Alhaji Abdul Aziz Mamud (Mai Turaka) ya zama mai taimakawa Sanata Barau Jibrin mataimakin shugaban majalisar tarayya
- Katsina City News
- 23 Jul, 2024
- 752
Katsina Times
Alhaji Abdul Aziz Mamuda (Mai Turaka) ya zama mai taimakawa mataimakin shugaban majalisar dattawa ta kasa, Alhaji Barau Jibrin. Kamar yadda jaridar Katsina Times ta ga takardar wannan aiki da aka bai wa Mai Turaka ta nuna aikin shi ya fara daga ranar hudu ga watan Maris 2024.
Takardar wadda kilak na majalisar dattawa ya saka ma hannu tana dauke da albashin da za a rika bai wa Mai Turaka duk wata. Katsina Times ta gano tuni Mai Turaka ya amshi wannan aikin da aka ba shi kuma ya cika duk ka'idar cikakken ma'aikaci a ofishin Barau Jibrin.
A kwanakin baya ne, gwamnatin Katsina ta fitar da sunayen membobi da shugabanni masu kula da wasu hukumomin ma'aikatun jihar Katsina. Sunan Mai Turaka ya fito a cikin membobin da suke hukumar kula da tsara birane na jihar Katsina.
Mai Turaka ya rika mukamin mai taimakawa gwamnan Katsina a wayar da kan jama’a, lokacin gwamnatin Aminu Bello Masari, matsayin da ya rike tsawon shekaru kafin su bar gwamnatin saboda karewar wa'adin shekaru takwas na gwamnatin Masari.
Mai Turaka ya kafa tarihi a siyasar Katsina, wanda ba za a taba mantawa da shi ba. Tarihin kuwa shine wanda ya yi sanadin da wasu manyan jiga-jigan PDP suka dawo APC. Daga cikin su akwai Barista Ibrahim Shema tsohon gwamnan Katsina da Alhaji Hamisu Gambo Dan Lawan Katsina ciki har da kwamishin kudin na jihar Katsina na yanzu da sauransu.
Mai Turaka dan kasuwa ne, kuma mai harkar sana’ar man fetur. Daga cikin ayyukan shi na alheri akwai taimakon kungiyoyin matasa da ciyarwa lokacin watan Ramadan.