Hisbah Zata Fara Sintiri Don Dakile Karuwanci a Katsina
- Katsina City News
- 23 Jul, 2024
- 489
Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta sanar da fara sintiri a birnin Katsina domin yakar ayyukan karuwanci. Wannan sanarwa ta fito ne a wata takarda mai dauke da sa hannun Babban Kwamandan Hukumar, Dr. Aminu Usman (Abu Ammar), mai dauke da kwanan wata 19 Yuli, 2024.
Sanarwar ta ce, "Wannan yunkuri yana bin umarnin da hukumar ta bayar na hana duk wani aikin fasadi a fadin jihar."
Hukumar ta bayyana cewa za a fara sintirin daga ranar 3 ga watan Agusta, 2024, inda za a gudanar da bincike da cafke duk wanda aka samu da laifin karuwanci. Hukumar ta gargadi jama’a da su dakatar da ayyukan fasadi domin kauce wa daukar matakin doka.
Dr. Usman Aminu ya ce za a bi ka'idojin da aka sanar wa ofisoshin su ko ta hanyar kafafen sada zumunta domin cikakken bayani. Ya kara da cewa duk wanda aka kama za a bi matakan doka yadda ya kamata.
Hukumar Hisbah ta ce za ta yi aiki kafada da kafada da jami'an tsaro domin kare martabar al'ummar Katsina da inganta tsaro a fadin jihar.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa duk wani aiki da aka gudanar za a yi shi ne domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Katsina.