Dattijuwa Mai Shekaru Saba’in 70 Ta Kammala Makarantar Qur'ani a Kano

top-news

Rabi Muhammad tana daya daga cikin daliban da suka kammala karatun Qur'ani a Kano. An gudanar da walima don bikin kammala karatunta na Ɗaliban. 

Rabi, mai shekaru saba’in, ta bayyana cewa ta fara karatun Qur'ani tun tana yarinya amma an cire ta daga makaranta saboda aurar da ita. Ta cigaba da karatu tare da taimakon almajirai da ke kusa da ita, da kuma 'yarta Maryam, wadda ta kasance malamarta.

Duk da kalubalen da ta fuskanta na rashin damar ci gaba da karatu saboda aure, Rabi ta samu damar ci gaba da karatunta lokacin da 'yarta ta kawo ta cikin shirin tallafi. Ta ce: "Da taimakon Allah mai girma, na yi shi. Na ji dadin shiga wannan makaranta, kuma da yardar Allah mai girma, na kammala karatun Qur'ani mai tsarki."

A lokacin bikin walima, Rabi ta bayyana farin cikinta da kammala karatun Qur'ani mai tsarki, tana mai cewa: "Alhamdulillah! Tun da aka sanar da ranar kammalawa, nake farin ciki da jin dadi."

Rabi ta kuma yi kira ga matasa da dattawa da su dage wajen neman ilimi, musamman karatun Qur'ani, tana mai cewa ba a taba tsufa wajen koyan karatu. Ta yi fatan alheri ga dukkan al’umma tare da rokon su dage wajen neman ilimi da karatun Qur'ani mai tsarki.

Mun dauko labarin a jaridar Daily Struggle ta harshen Turanci