Tatsuniya Ta 40: Wata Mata Da Aljani
- Katsina City News
- 20 Jul, 2024
- 572
Ga ta nan, ga ta nanku.
An ce wata mata a wani ƙaramin ƙauye ta jima tare da mijinta amma ba su sami haihuwa ba. Sun nemi maganin samun haihuwa, amma ba su sami biyan buƙata ba, sai suka yi haƙuri.
Ana nan, wata rana matar ta je gona tana noma, sai ta ji kukan yaro a gindin wata bishiya. Da ta matsa kusa, sai ta ga wani jariri a cikin tsumma. Sai ta ɗauke shi ta goya, ta kuma ɗauki fartanyarta, ta koma gida. Da mijinta ya dawo sai ta ɗauko jariri ta kawo masa, ta ce da shi: "Da ma ina da kwantaccen ciki, shi ne yanzu ka ga na haihu a gona."
Mijin ya yi shiru, yana tunani, sai ya ce: “Anya kuwa ke ce kika haifi jaririn nan?" Ta dage cewa ita ce ta haife shi. Sai ya ce: "To mun gode wa Allah."
Suka ci gaba da renon yaro, amma duk sanda suka je gona da shi sai ya yi kuka ya hana su aiki. Da matar ta ga haka na faruwa kullum, sai ta je cikin danginta ta ɗauko kanwarta domin ta riƙa renonsa idan sun tafi gona ita da mijinta.
Wata rana mai gida da matar suka tafi gona suka bar yaro a hannun mai reno, mai renon ta ga yaron ya rikida, ya zama babban mutum, sai ya yi aman 'yan mata goma sha biyu. Ya buɗe rumbu, kuma ya fito da hatsi suka susuka suka nika, sai ya kwashe garin ya barbaza shi a tsakar gidan; sai kuma ya haɗiye 'yan matan, ya rikida ya koma ƙaramin yaro.
Can da mai gida da matar suka dawo, suka ga barnar da aka yi musu, sai matar ta kama kanwarta da duka wai ta yi mata barna. Yarinya ta ce ba ita ba ce, yaron ne. Sai yayarta ta ce: "Ta yaya wannan ƙaramin yaro zai buɗe rumbu, ya ɗebo hatsi, ya susuka shi, ya nike ya zubar?" Ba su dai yarda da bayanin yarinyar ba. Haka dai, kullum idan sun fita sai ya yi wata barna, kuma sai matar nan ta doka kanwarta.
Wata rana matar ta kama kanwarta tana duka a kan barnar da yaron ya yi, sai wata tsohuwa ta kira ta ta ce mata: "Wannan duka da kike yi wa kanwarki fa ba ta da laifi. Wannan yaron da yake gidanku ba ki sani ba tsohon aljani ne kika kawo gidan." Mamaki da tsoro suka kama matar, amma sai tsohuwar ta ci gaba da bayaninta tana cewa: "Idan kina so ki tabbatar, gobe kada ku je gona; bayan gari ya waye ku fita ku ce za ku je gona; sai ku zo ku buya a gidana, za ku ga komai da idanunku."
Sai ta ce: "To. Allah ya nuna mana goben."
Da gari ya waye mijin da matar suka shirya, kamar za su je gona. Da suka fita sai suka buya a gidan tsohuwa. Bayan wani dan lokaci sai suka ga yaron ya rikida, ya zama babba, suna gani ya buɗe bakinsa ya yi aman 'yan mata goma, nan da nan ya hau rumbu ya buɗe ya ɗebo hatsi, nan take 'yan matan suka susuka hatsin, suka nike shi, suka shiga watsar da garin a cikin gida, suna yi suna waka. Da matar ta ga abin da yaron ya yi sai ta gaya wa mijinta gaskiya da cewa, ai da ma ba danta ba ne, kuma a gona ta tsince shi. Sai mijin ya ce: "Tun farko da ma na yi shakka, ga shi ta tabbata karya kika yi mini."
Sai ta fadi tana kuka, ta shiga hurwa tana ba shi haƙuri, ta ce: "Ai da wannan da, gara mu zauna babu."
Da tsohuwa ta ga abin da ke gudana tsakanin mijin da matar, sai ta ce: "Yanzu abin da za ku yi domin ku rabu da wannan masifa shi ne, ku samo akuya da kwaikwaye guda bakwai, sai ku ce za ku je ganin gida. Bayan kun kama hanya kun shiga daji, sai ku sami gindin tsamiya ku ce za ku huta. Idan kun shimfiɗe yaron sai ku ajiye kwaikwayen nan bakwai a gefensa ku daure akuyar a jikin tsamiyar. Can sai ku ce kun yi mantuwa." Ta ce da su: "Kuna jin abin da nake faɗa?"
Suka ce: "Muna ji sarai."
Ta ci gaba da ce wa matar: "Ki ce za ki koma gida ki ɗauko abin da kika manta. Daga nan kada ki dawo. Jim kaɗan shi ma mijinki sai ya ce zai bi sawunki saboda kin jima. To idan kun tafi kada ku koma; da zarar kun jima zai tashi ya tafi abinsa." Sai suka yi wa tsohuwa godiya suka koma gida.
Da gari ya waye sai matar nan da mijinta suka ce za su je ganin gida, sai suka samo duk abubuwan da tsohuwa ta ce su nemo. Da lokacin tafiya ya yi sai suka kama hanya har suka isa gindin wata tsamiya, sai mijin ya ce ya kamata su huta a nan; suka daure akuya a gindin bishiya suka zauna, can sai mijin ya ce: "Kash!, mun yi mantuwa."
Sai matar ta ce: "To bari in je in ɗauko."
Mijin ya ce: "To gara ki yi sauri."
Bayan matar ta tafi, sai ya ce ta dade, bari ya bi sawunta. Shi ma ya tashi ya bar wurin. Da ya yi nisa sai ya buya. Yana nan yana kallon gindin tsamiya, can sai ya ga yaro ya rikida ya zama tsoho tukuf da sanda; sai ya kunce akuyar, ya riƙe a hannunsa; kuma ya ga ya ɗebi kwaikwayen nan bakwai ya kama hanya ya shiga ƙungurmin daji. Da mijin nan ya ga haka sai shi ma ya juya, ya kama hanyar gida.
Kurunkus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Karya da ha'inci: masifu ne da ke iya bata zaman da aka dade cikin amana.
- Neman afuwa da lafiya: su ne kadai ke iya magance matsala a zaman amana.
- Tsintacciyar mage ba ta yin kyanwa:
- Karya fure take, ba ta 'ya'ya.
Daga Littafin Taskar Tatsuniyoyi Na Dakta Bukar Usman