Noma Ya Gagara a Wasu Yankuna a Faskari

top-news

An hana su biyan miliyan 15 don su yi noma, sun kashe sama da miliyan 40 don biyan kudin fansa.

 Daga: Awwal Jibrin Faskari, Katsina Times

Sakamakon rashin tsaro a Gundumar Mazabar 'Yankara dake karamar hukumar Faskari, kashi ɗaya ne cikin huɗu suka samu damar yin shuka. A gonaki, inda har yanzu kashi uku ba su san ranar yin shuka ba, sakamakon rashin tsaro a gudumar mazabar 'Yankara.

Da farkon damina, kamar lamarin tsaron ba zai ta'azara ba. Domin kuwa har an fara shiri da maharan daji inda suka nemi a basu naira miliyan sha biyar (₦15,000,000) don a kyale kowa ya je gona inda yake so, da kuma sharadin ba za su sake shiga cikin gari su ɗauki wani ba. Wasu suka ɗauki gabarar tara kudin dan a kai musu.

Ana cikin haka ne kwatsam jami'an tsaro suka samu labari suka hana hada kudin da ba barayin daji. Inda suka tsoratar da duk wanda aka samu da hannu wajen hada kudin zai dandana kudarsa.

Rashin hada kudin ya sa barayin daji sun hana zuwa gona. Kuma duk wanda ya je gona in ba Allah ya tsare ba, ko dai a ɗauki mutum ayi garkuwa da shi sai an kai kudin fansa, ko su harbi mutum.

Zuwa yanzu a kalla an yi asarar sama da miliyan 40, kuma ba a san inda matsalar za ta tsaya ba. Yanzu haka akwai mutane a hannun barayin daji. Ko a ranar Talata 9/7/2024, barayin sun harbi mutane a gonakinsu dake yankin 'Yankara. Mutum biyu sun mutu wasu sun jikkata. Har zuwa rubuta wannan rahoton, ba mu samu bayanin daga jami'an tsaro ba.

NNPC Advert