Gwamnan Katsina Ya Taya Sheikh Dahiru Bauchi Murnar Cika Shekara 100
- Katsina City News
- 09 Jul, 2024
- 494
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda PhD, ya taya babban malamin addinin Musulunci kuma jagoran Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, murnar cika shekaru 100.
Gwamna Radda, cikin sakon taya murnarsa, ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin "babban malami a duniyar Musulunci, wanda ya kware wajen sanin Alkur'ani mai tsarki, Hadisi, Fiqhu, da kuma fahimtar ilimin sufanci wanda ya bambanta shi a matsayin jagora.
Gwamnan ya kara da cewa, "Koyarwar Sheikh Dahiru Bauchi ta ketare zamani, ta bunkasa rayuwar mutane da dama ta hanyar fahimtar Alkur'ani mai tsarki da yake yi. A tsawon rayuwarsa, ya kasance ginshiki da jagorar kyawawan halaye a cikin al'ummarmu."
Yayin da yake yaba da gudunmuwar Sheikh Dahiru Bauchi wajen bunkasa ilimin addini da jagoranci a Arewa da musamman Jihar Katsina, Gwamna Radda ya jinjina masa bisa dagewarsa wajen yada ilimi da hada kan Musulmai.
"Muna murnar wannan gagarumin lokaci, muna kuma tunawa da dimbin albarkar da Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya kawo wa al'ummarmu ta hanyar hikimarsa, koyarwarsa, da jagorancinsa na koyi," in ji Gwamna Radda. "Gadonsa na ilimi da jagoranci zai ci gaba da zama abin koyi ga al'umma masu zuwa."
Gwamnan, a madadin gwamnatin da mutanen Jihar Katsina, ya yi addu'ar Allah ya ci gaba da ba Sheikh Dahiru Bauchi lafiya, hikima, da albarka yayin da ya shiga karni na biyu na rayuwarsa.