Tinubu ya ƙirƙiro da sabuwar ma'aikatar gwamnatin taraiya

top-news

Shugaban ƙasa Bola Ahmed h-Tinubu ya kirkiro ma’aikatar kula da kiwon dabbobi.

An sanar da samar da ma’aikatar ne a yayin kaddamar da kwamitin aiwatar da gyara harkokin kiwon dabbobi da aka kafa domin magance matsalar manoma da makiyaya.

Wadanda suka halarci bikin kaddamarwar sun hada da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, da sauran mambobin majalisar zartarwa.

A tuna cewa, a watan Satumba, 2023, Shugaba Tinubu, ya amince da kafa kwamiti domin sake fasalin sana’ar kiwo da kuma samar da hanyoyin magance tashe-tashen hankula da ke faruwa a kasar nan.

Hakan ya biyo bayan gabatar da wani rahoto daga babban taron kasa kan sauye-sauyen kiwon dabbobi da magance rikice-rikice masu nasaba da juna a Najeriya.