Yarjejeniyar tallata auren madigo da liwadi: Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar karar jaridar Daily Trust
- Katsina City News
- 06 Jul, 2024
- 449
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta maka jaridar Daily Trust a kotu, tare da shigar da korafi game da ita, a gaban ƙungiyar masu gidajen jarida ta Najeriya saboda abin da ta kira ''yaɗa kalaman neman tayar da rikici da karya aikin jarida''
Ministan yaɗa labaran Najeriya, Mohammed Idris ya ce gwamnatin tana sane da yadda a cikin ƴan watannin baya, jaridar Daily Trust ke yada labaran da ke neman gogawa gwamnatin kashin kaji.
Da ya ke magana a wajen wani taron manema labarai a yau Asabar, ministan yada labaran ya kafa hujja da labaran da jaridar Daily Trust ta wallafa a game juyin mulkin Nijar, da wanda ya ce jaridar ta rubuta a kan shirin sauya sunan titin Murtala Muhammad da ke Abuja zuwa Wole Soyinka da kuma na baya bayan nan a game da sanya hannu a kan yarjejeniyar da ta shafi amincewa da auren jinsi.
Ya yi bayanin cewa a dukkan labaran, gwamnatin ta gano yadda jaridar ta bayar da rahoto ba tare da gabatar da hujja ko shaidun zargin da ta yi ba, lamarin da kuma gwamnatin ke kallo a matsayin wani yunƙuri na wallafa ƙarya domin tunzura jama’a.
Ya ce: ‘’Ba mu taɓa tunanin Daily Trust da mutanen da ke da ita za su kai wannan mataki ba wajen neman tayar da rikici a ƙasar nan, ta hanyar zargin cewa gwamnati ta sanya hannu a kan yarjejeniyar tallata auren jinsi. Wannan tsabar zalumci ne saboda babu wannan tanadi a cikin yarjejeniyar.’’
Ministan ya koka da yadda wannan labarin ya janyo huɗuba mai zafi daga wasu malaman addini da kuma jefa jama’a cikin halin ɗar-ɗar, wanda kuma ya ce jaridar ce ta janyo.
Saboda haka, ministan ya ce ‘’Gwamnatin tarayya za ta bi duk hanyoyin da doka ta amince da su, domin neman haƙƙi a kotu.’’