Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Bayyana Cewa Sultan Na Sokoto Bai Da Iko Na Doka Don Yin Nade-nade
- Katsina City News
- 02 Jul, 2024
- 499
A yayin sauraron ra'ayi na jama'a kan dokar kananan hukumomi da sarauta ta 2008 a jihar Sokoto, kwamishinan shari'a, Barista Nasiru Binji, ya bayyana cewa dokar sarauta ta yanzu a jihar ba ta dace da kundin tsarin mulkin Najeriya ba.
Ya ce, "Sashe na 5(2) na kundin tsarin mulki ya tanadi cewa ikon gudanarwa na yin nade-nade a jiha yana hannun Gwamna kai tsaye ko ta hannun mataimakinsa, kwamishinoni ko wani wakilin gwamnati da Gwamna ya nada.
"Saboda haka, ba a baiwa majalisar sarkin ikon yin nade-nade ba. Sashe na 76(2) na dokar kananan hukumomi da sarauta ta Sokoto ya baiwa majalisar sarkin ikon nada dagatai da hakimai a jiha amma tare da amincewar Gwamnan da ke kan mulki.
"Saboda haka, wannan sashe ba ya jituwa da kundin tsarin mulki na 1999 da aka yi wa gyara kuma ba zai iya tsayawa ba. Domin ikon yin nade-nade ikon gudanarwa ne kuma waye ke gudanar da ikon? Ba Gwamna ba ne? Wannan shi ne dalilin gyaran doka. Don gyara kuskuren da aka yi a baya."