Comrade Rafukka Ya Fito Takarar Shugaban Matasan PDP a Jihar Katsina
- Katsina City News
- 28 Jun, 2024
- 469
A ranar Alhamis, 27 ga watan Yuni, Dan Gwagwarmaya Comrade Usman Husaini Rafukka ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban matasa na jam'iyyar PDP a jihar Katsina.
Comrade Rafukka ya bayyana cewa dalilinsa na tsayawa takarar ba don kashin kansa ba ne, sai don amfanin matasan jihar Katsina.
Mai rikon mukamin Kakakin jam'iyyar PDP na jihar Katsina, Alhaji Lawal Dan'ade, ya bayyana dalilai guda shida da suka sa yake ganin Usman Rafukka ya cancanci jagorancin matasa a cikin jam'iyyar PDP. Ya lissafta gaskiya, rikon amana, gwagwarmaya, girmamawa, rashin tsoro, da kin zalunci. Yace, "Na tabbatar da gaskiyar abinda na fada game da Usman a wurare daban-daban."
A nasa jawabin, shugaban riko na jam'iyyar PDP na karamar hukumar Katsina, Alhaji Ibrahim Galadima, ya ja hankalin Comrade Rafukka da ya ci gaba da nuna gaskiya da rikon amana da aka san shi da su. Har ila yau, ya jaddada goyon bayansa ga Usman a wannan gwagwarmaya, inda ya ce ya cancanci riko da kowane irin mukami, ba kawai na shugaban matasa ba.
Taron da aka gudanar a yankin wakilin Kudu 3 ya samu halartar 'ya'yan jam'iyyar PDP na yankin, shugaban jam'iyyar PDP na wakilin Kudu 3, da shugaban sashin kudi na riko a jam'iyyar PDP a jihar Katsina, matasa da sauran masu fada aji a cikin jam'iyyar.