Tatsuniya Ta 32: Labarin Binta 'Yar Sarki
- Katsina City News
- 22 Jun, 2024
- 760
Ga ta nan, ga ta nanku.
An yi wani Sarki a wani gari mai mata biyu, kowacce tana da 'ya. Yarinya ɗaya sunanta Binta, ɗayar kuma Falmata. Sarki yana ji da 'ya'yan nan nasa, to amma fa ya fi son Binta don ita ce ƙarama, kuma 'yar amarya.
Ana nan, rannan sai Sarki ya tafi wani gari mai nisa, kuma zai daɗe a can. Bayan ya tafi da 'yan kwanaki, sai ciwo mai zafi ya kama amaryarsa, watau mahaifiyar Binta. Da ta lura ciwon kamar ba wanda za ta tashi ba ne, sai ta kira kishiyarta ta gaya mata cewa tana jin ba za ta tashi ba, amma idan ta cika, tana rokon ta ta kula da 'ya'yansu cikin amana. A cikin tausayi kishiyar ta ce da ita: "Zan yi bakin ƙoƙarina in kula da su."
Bayan kwana biyu da yini ɗaya, sai amaryar Sarki ta rasu. Sarki dai bai dawo daga tafiyar da ya yi ba har wasu 'yan kwanaki suka wuce.
Rannan sai kishiyar uwar Binta ta sa ta ɗauko ruwa a rafi a cikin wani masaki, kuma ta gaya mata lallai a rafin Apko mai cinye mutane za ta ɗebo ruwan, watau ba a ɗaya rafin mai lafiya ba. Wancan rafin mai lafiya wanda daga shi mutanen garin suke ɗaukar ruwa sunansa Diddire.
Binta ta ɗauki masaki ta garzaya wajen kabarin mahaifiyarta, tana kuka tana waka, tana cewa:
"Baba, baba, babar Binta,
Kishiyarki ta ce in je Apko in ɗebo ruwa,
In je Apko ko in je Diddire?"
Daga cikin kabarin sai ta ji mahaifiyarta ta amsa mata da waka tana cewa:
"Ki je Diddire,
Kada ki je Apko,
Domin Apko zai Apka da ke."
Binta ta tafi rafin Diddire ta ɗebo ruwa. Da kishiyar uwarta ta ga ba ta ɗebo ruwan Apko ba, sai ta hau ta da duka. Ta ma zubar da ruwan da ke cikin masakin, ta ce lallai maza ta je ta ɗebo mata ruwa daga kogin Apko, kuma ta gaya mata cewa idan ta kuskura ta ɗebo mata ruwan Diddire, to za ta yanka ta.
A kan dole Binta ta ɗauki masakin ta tafi rafin Apko dibar ruwa. Tana shiga za ta ɗebi ruwan, sai rafin ya cinye ta. Tana nan a cikin ruwa, har wasu 'yan kwanaki. Ita kishiyar uwarta ba ta sa an je nemanta ba, kuma ita ba ta ɓoye ba. Ko fadawa ma ba ta gaya wa ba, har ranar dawowar Sarki. A ranar da Sarki ya dawo sai fadawa da jama'ar gari suka fita bayan gari suna yi masa maraba da zuwa. Masu tambura suka goce da kida, ana yi masa kirari ana cewa: "Baban Binta ya dawo, Sarki baban Binta ya dawo."
Da Binta ta ji ana buga tambarin babanta, ga shi kuma ba za ta iya fita daga ruwan ba, sai ta kama kuka da waka tana cewa:
"Falmata ce 'yar Sarki,
Babanta ya dawo,
Falmata kin ji daɗi,
Falmata 'yar Sarki."
Sarki ya sa ido ko zai ga Binta a cikin masu tarye, amma bai gan ta ba, kuma ya saba idan ya yi tafiya ya dawo akan ɗoro ta a kan doki, a kai ta gabansa, su gaisa. Ya sake dubawa bai ga Binta ba sai Falmata. Sai hankalinsa ya tashi, har dai ya kasa daurewa ya tambayi fadawansa inda Binta take. Sai suka ce ai Binta ta bace, ba wanda ya san inda take. Suka ƙara da cewa ai ma yau kwana goma sha tara ke nan da uwarta ta rasu. Hankalinsa ya tashi, amma ya yi ta maza, ya shanye halin damuwar da yake ciki.
Da ya shiga gida, sai ya kira uwargidansa, ya tambaye ta inda Binta ta je. Sai ta ce ba ta sani ba, tun da dai ta fita yawo ba ta sake komawa gida ba. Yana jin haka, sai ya sa aka shiga neman Binta. Wasu daga cikin masu nemanta suka bi ta rafin Apko.
Da fari ba su ga alamun kowa a can ba, to amma daga baya sai suka ji muryar mutum na waka a cikin rafin. Da suka kasa kunne da kyau, sai suka ji ana waka ana cewa:
"Ya 'yan'uwa kada ku zo Apko,
Idan kun zo zai Apka da ku,
Ni kishiyar uwa ta aiko ni nan,
Har ya Apka da ni."
Da masu nemanta suka ji haka sai kawai suka koma suka shaida wa Sarki abin da suka jiyo a kogin Apko. Sai Sarki ya ce da su da sauran fadawansa su je tare da shi bakin rafin ya ji.
Nan da nan suka dunguma, kuma suka tarar Binta tana yin wannan wakar. Sarki ya kasa kunne, kuma daga ƙarshe dai ya fahimci cewa murya Binta ce. Sai nan da nan ya ce da Sarkin maroka ya shiga gari ya yi yekuwa cewa duk wanda ya fito da Binta daga kogin Apko za a ba shi dawaki da dukiya mai yawa.
Da fari ba wanda ya ce zai gwada, amma can sai wani tsoho ya zo ya ce zai shiga ruwan ya tsamo ta.
Sai wasu mutanen garin suka ce: "Amma tsohon nan da rigima kake."
Sai Sarki ya ce: "A bar shi ya gwada."
Tsoho ya faɗa ruwa, zuwa wani ɗan lokaci sai ya fito da Binta a hannunsa.
Da Sarki ya ga 'yarsa sai ya ji kamar ya zabura da gudu ya rungume ta saboda murna da farin cikin da yake ciki. Amma sai ya nuna halin manya, ya jure.
A cikin murna da farin ciki Sarki da fadawansa da jama'arsa suka yi ta gode wa tsohon nan. Da aka koma fada ya sa aka kwanto dawakan Asbin da kili da fari da ja da baki da ingarma da kuru da dai dawaki iri-iri masu yawa da dukiyar da ba a taɓa ganin irinta ba a ƙasar, aka ba tsoho.
Bayan an tashi daga zaman fadanci Sarki ya shiga turakarsa, sai ya kira matarsa da Falmata, ya tambaye su yadda aka yi Binta ta faɗa ruwa. Sai suka yi shiru. Da dai ya gane munafunci suka yi, sai ya kore su, ya ci gaba da rayuwarsa da 'yarsa Binta. Shi ya sa duk wanda ya je garin zai ji ana cewa: "Binta 'Yar Sarki."
Kurunkus.
TUSHE: Mun ciro wannan labarin daga Littafin "TASKAR TATSUNIYOYI" Na Dakta Bukar Usman.