Mutanen Bayelsa Sun Gididdibe wani kifi mai fama da rashin lafiya da ya makale a bakin Teku.
- Katsina City News
- 20 Jun, 2024
- 304
Mutanen al'ummar Okpoama a karamar hukumar Brass ta jihar Bayelsa sun yanka wani kifi da aka samu a bakin tekun Atlantic. An kiyasta kifin yana da tsawon mita 15 kuma an gano shi ne a daren Talata.
City & Crime ta ruwaito cewa lokacin da mutanen yankin suka ga kifin a safiyar Laraba, sun ruga bakin teku da takuba, wukake, da gatari domin yanka kifin don nama. Tarinyo Akono, tsohon shugaban kungiyar 'yan jaridu ta Nigeria (NUJ) a jihar Bayelsa, kuma dan asalin yankin, ya bayyana cewa kifin ya mutu ne bayan ya makale saboda ruwan kasa. Ya kara da cewa da an gano kifin yana da rai a da, da za a iya ceto shi a mayar da shi tekun.
Engr Seiyefa Felix Ben-Basuo, shugaban matasa na al'ummar Okpoama, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce mutanen yankin suna bakin teku suna sarrafa kifin don nama. Ya kuma ambaci wani lamari makamancin wannan a watan Agusta na shekarar 2019, lokacin da wani babban kifi ya makale kuma aka yanka shi.