Shi Almajiri da Mabaraci wanne ne yake matsalarmu a Arewa? - Al-Amin Isa
- Katsina City News
- 19 Jun, 2024
- 598
ALMAJIRI: Ita wannan kalma ta Almajiri, Bahaushe ya aro kalmar ne daga kalmar larabci “al-muhajir” wadda take nufin wanda yayi Hijira. Nakasa samun gamsasshiyar amsa miyasa Bahaushe ya zaɓi yakira mai neman ilmi al-muhajir maimakon tālib wadda tafi kusa da ma’anar abinda yakeyi. Domin akwai banbanci tsakanin kalmar al-muhajir da kuma tālib wadda take nufin ɗalibi. Kalmar tālib itace tafi dacewa da wanda ke neman ilmi domin shi al-muhajir yanada dalilai nayin hijira ba dole neman ilmi ba kawai. Wani bayanin na nuna cewar turawan mulkin mallaka ne suka laƙabawa masu neman ilmin addini almajiri sukuma ʼyan Boko suka kirasu da ɗalibai.
BARA: Hanya ce da mai yinta yake amfani da wasu kalmomi domin yin ishara kan halin da yake ciki don ayi mashi taimako. Wannan kalmar Bahaushe yasamota ne daga kalmar larabci ta “Barakah” watau albarka da Hausa sai Bahaushe ya datseta yamaida ita Bara. Bara tana nufin mai neman albarka, masu ba mabaraci kuma suna neman albarka ne gun ubangiji shiyasa suke bada taimako watau “sadaka”. Bara bata cikin al’adar Bahaushe domin baƙuwar al’ada ce wurinshi. A al’adar Bahaushe yasan yatashi yanemi na kanshi, amma mu’amalarshi data shigo tsakanin Bahaushe da wasu baƙin ƙabilu yasa yasami mutuwar zuciya har yakoyi bara.
Abin tambaya anan shine tsakanin Almajirci da Bara wannene matsalarmu yanzun a Arewa?