Gwamnan Zamfara: "Ba Zamu Shiga Sulhu da 'Yan Bindiga Ba"
- Katsina City News
- 14 Jun, 2024
- 473
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa shiga sulhu da 'yan bindigar da ke haddasa ta’addanci a jihar ba.
A ranar Laraba, gwamnan ya halarci wani gangami da matasan Zamfara suka shirya mai taken 'Tafiyar Zaman Lafiya'. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa wata gamayyar matasan Zamfara sun shirya tattaki domin samar da zaman lafiya da haɗin kai, domin murnar zagayowar Ranar Dimokuraɗiyya.
Ya ƙara da cewa an fara wannan gangami ne daga gidan gwamnatin jihar, wanda kuma aka ƙare a dandalin Freedom, inda dubban mutane suka taru domin nuna goyon bayansu ga gwamnati a yaƙin da take yi da ’yan bindiga.
Da yake gabatar da jawabinsa, Gwamna Lawal ya bayyana cewa a shirye yake ya yi duk wani yunƙuri domin ganin an dawo da zaman lafiya a dukkan sassan Jihar Zamfara.
“Ina so in gode wa ƙungiyar haɗin gwiwar matasa da suka shirya irin wannan muhimmin ‘tattakin zaman lafiya’ saboda muna buƙatar irin wannan shiri a wannan mawuyacin lokaci.
“Muna da dogon tarihi na kasancewa mutane da jiha masu zaman lafiya. Duk da haka, a cikin 'yan shekaru, abubuwa sun canja sosai. Wannan yana buƙatar nazari don ganin inda muka yi kuskure da yin gyare-gyaren da suka dace. Tsaro alhakin kowa ne; dole ne mu bada haɗin kai da goyon bayan tsarin.
“A koyaushe ina maimaita cewa; babu wani abu wai shi "sulhu" da 'yan ta'adda, mun ga yadda gwamnatocin baya suka yi yunƙurin sasantawa, wanda hakan ya ƙara wa ’yan bindiga ƙwarin gwiwa.
“A wannan Ranar Dimokuraɗiyya, kuma da bukukuwan Sallah, ina mai farin cikin sanar da cewa na amince da biyan albashin watan Yuni ga ma’aikatan jihar Zamfara. Baya ga albashin, mun cika alƙawarin da muka ɗauka na aiwatar da mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 30, saɓanin yadda aka saba da dubu bakwai.
“Zan ci gaba da aiki don ci gaban jiharmu da kuma tallafa wa mutanenmu. Mun samu ci gaba sosai a fannin tsaro, ilimi, noma, kiwon lafiya, samar da ababen more rayuwa da ƙarfafawa da dai sauransu.
“Da wannan zaman lafiya, mun aike da saƙo mai ƙarfi ga maƙiyan jihar cewa mun haɗa kai a matsayinmu na al’umma, kuma gwamnati ta jajirce wajen ganin ta kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga a Jihar Zamfara.”