MASARAUTAR KANO: Umarnin Shigowa Kano don Bikin Hawan Babbar Sallah
- Katsina City News
- 11 Jun, 2024
- 754
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A yau, Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi, ya bayar da sanarwa ga dukkan Hakimai na masarautar Kano cewa su shigo cikin Birnin Kano domin bikin Hawan Babbar Sallah. Wannan umarni yana nuni da cewa dukkan Dagatai, Mahayansu, da Dawakansu su halarta a ranar Juma'a, 14 ga watan Yuni, 2024, wanda ya yi daidai da 8 ga watan Zhulhija 1445AH.
Haka kuma, an umarci Hakimai da su zo Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a ranar Asabar, 15 ga watan Yuni, 2024, wanda ya yi daidai da 9 ga watan Zhulhija 1445, da misalin karfe 11:00 na safe. Wannan taro zai kasance don karbar umarni kai tsaye daga Sarkin Kano ba tare da bata lokaci ko makara ba.
Bayan wannan taro na Majalisa, za a gudanar da wani taron na musamman a Dakin Taron Majalisar Masarautar Kano dake gidan Nassarawa. Wannan taro zai ba da damar yin cikakken bayani kan yadda bikin Hawan Babbar Sallah na bana zai kasance.
Hakazalika, an sanar da Shugaban Karamar Hukumar Kano domin tabbatar da dukkan tsare-tsaren da za su taimaka wajen shigar Hakimai cikin birni don wannan biki mai muhimmanci.
Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, wanda shi ne Babban Mashawarci, ya tabbatar da cewa dukkan Hakimai su bi wannan umarni don tabbatar da an gudanar da bikin cikin nasara.