Tatsuniya Ta 26: Labarin Rimi da 'Yar Amana
- Katsina City News
- 09 Jun, 2024
- 364
Ga ta nan, ga ta nanku.
An yi wani gari mai yawan jama'a da Sarkinsu mutumin kirki. Akwai wani mutum mazaunin wannan gari tare da matarsa da 'yarsu daya. Suna nan cikin farin ciki har sai wata rana ciwon ajali ya kama matar wannan mutum. Kafin ta rasu, sai ta kira mijinta ta ce: "Mai gida, ina jin ba zan tashi daga ciwon nan ba. Ga amanar 'yarmu nan, ka kula da ita sosai. Kada ka bari wani mugun abu ya same ta."
Mijin ya amsa mata da alkhairi. Da matar ta rasu, sai uban yarinyar ya ci gaba da renonta har ta yi wayo. Sai wata rana shi ma ciwon ajali ya kama shi. Bai san yadda zai yi da 'yarsa ba, kuma ba shi da kowa a garin. To amma akwai wata tsohuwar bishiyar rimi a kofar gidansa, sai ya fito ya dauko yarinyar ya kai ta gindin rimin. Sai ya dubi rimin ya ce ya ba shi amanar 'yarsa domin yana jin wa'adinsa ya kusa cika. Daga nan ya koma gida, bai sake fitowa ba, har ya rasu.
Bayan rasuwarsa da 'yan kwanaki, duk sanda yarinya ta ji yunwa sai ta je wurin rimin ta kama waka tana cewa:
"Rimi, rimi uwata,
Rimi ubana ya ba ka amanar Allah,
Uwata ta ba ka amanar Allah."
Da ta yi wannan waka sai rimi ya ba ta abin da take so. Kullum haka sai wata rana Gizo ya fita yawo sai ya ga 'yar budurwa tana wanki a gindin rimi. Sunanta Jummai. Da Gizo ya ga kyaunta sai ya garzaya gidan Sarki. Ya sami Sarki a fada tare da fadawansa, ya fadi ya yi gaisuwa ya ce da Sarki: "Sarki, Sarki kunnenka nawa?"
Sai Sarki ya ce da Gizo: "Biyu."
Shi kuma Gizo ya ce: "Kara biyu ka sha labari."
Sai Sarki ya yi murmushi ya dubi Gizo ya ce: Na kara."
Da Gizo ya sami yadda yake so, sai ya kwashe labarin Jummai ya gaya wa Sarki.
Da Sarki ya ji haka sai ya tura fadawansa su dauko yarinya. Da suka isa wurin rimi sai yarinyar ta gan su, kuma ta razana ta je ta rungumi rimi ta fara waka tana cewa:
"Rimi, rimi uwata, rimi ubana,
Uwata ta ba ka amanar Allah,
Ubana ya ba ka amanar Allah."
Sai rimi ya ce:
"Yi wankinki,
Yi wankinki,
Yi wankinki Jummai,
Cikin dari da goma,
Daya ya koma,
Cikin dari da goma,
Daya ya koma."
Da dogarai suka matsa sai duk suka mutu. Da Sarki ya ji labari sai ya sa a je a sare wannan rimi. Da aka taru za a sare, idan aka sara jikin sai ya sake tohowa. Idan an sake sara ma haka, har dai masu saran suka gaji, suka hakura. Har yanzu wannan rimi da ya rike amana yana can a garin, mutane suna zuwa kallon sa.
Kurunkus.
Tushe:
Mun ciro wannan labarin daga Littafin TASKAR TATSUNIYOYI na Dakta Bukar Usman.