EFCC Ta Sake Gurfanar Da Tsohon Shugaban SMEDAN, Masari Kan Zargin Karkatar da Kudi Naira Miliyan 119

top-news


Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta sake gurfanar da tsohon Darakta Janar na Hukumar Raya Kanana da Matsakaitan Masana’antu ta Najeriya (SMEDAN), Bature Umar Masari, a ranar Alhamis, 23 ga Mayu, 2024, bisa zargin Karkatar da Naira miliyan 119, 507,080.

An gurfanar da Masari ne a gaban Mai shari’a O.A Egwuatu na Babban Kotun Tarayya dake Maitama, Abuja, bisa tuhumar da aka sabunta na karin zarge-zarge 22.

Lauyan masu kara, Ekele Iheanacho, ya shaida wa kotu cewa an gabatar da sabuwar tuhumar a ranar 13 ga Mayu, 2013, kuma an mika ta a ranar 17 ga Mayu, 2019. Ya roki kotu ta karanta tuhume-tuhumen ga wanda ake tuhuma domin ya amsa laifinsa.

Tuhuma ta 19 na cewa: “Kai Bature Umar Masari tsakanin 27 ga Yuni, 2014 da 17 ga Yuli, 2014 a Abuja cikin ikon wannan kotu mai daraja ka yi amfani da kudin Naira miliyan 10 da aka biya a asusun bankin Diamond Bank Plc No. 002688674 daga kamfanin Rahuse Ventures Limited, lokacin da ka kamata ka san cewa kudin haramtattun ayyuka ne, wanda ya saba wa Sashe na 15(2)(d) na Dokar Hana Wanke Kudi ta 2011 da aka gyara ta Dokar No. 1 na 2012) kuma za a yi maka hukunci bisa Sashe na 15(3) na wannan doka.”

Tuhuma ta 20 na cewa: “Kai Bature Umar Masari tsakanin 14 ga Yuli, 2014 da 21 ga Yuli, 2014 a Abuja cikin ikon wannan kotu mai daraja ka yi amfani da kudin Naira miliyan 10 da aka biya a asusun bankin Diamond Bank Plc No. 002688674 daga kamfanin Rahuse Ventures Limited, lokacin da ya kamata ka san cewa kudin haramtattun ayyuka ne, wanda ya saba wa Sashe na 15(2)(d) na Dokar Hana Wanke Kudi ta 2011 da aka gyara ta Dokar No. 1 na 2012) kuma za a yi maka hukunci bisa Sashe na 15(3) na wannan doka.”

Bayan an karanta tuhume-tuhumen ga wanda ake tuhuma, ya musanta dukkansu.

Lauyan masu kara, bisa la’akari da musun laifin, ya nemi ranar fara shari’a. Amma lauyan wanda ake tuhuma, Okechukwu Edeze, ya roki kotu ta bar wanda yake karewa ya ci gaba da amfana da belin da aka ba shi tun a gaban Mai shari’a Okong Abang, wanda aka daga zuwa Kotun daukaka kara.

Edeze ya tabbatar da cewa wanda yake karewa yana bin ka’idojin belin tun daga ranar 24 ga Mayu, 2019.

Lauyan EFCC bai yi jayayya da bukatar ba, amma ya nemi kotu ta tabbatar da cewa masu bayar da beli suna nan kuma suna shirye su ci gaba da tsayawa wanda ake tuhuma.

Bayan sauraron dukkan hujjoji, Mai shari’a Egwuatu ya saki wanda ake tuhuma ga lauyansa kamar yadda aka roka, kuma ya dage shari’ar zuwa 16 ga Yuli, 2024, domin fara shari’a.